APC, PDP, da Sauransu: Abubuwa 8 da Ya Kamata Ku Sani game da Siyasar Jihar Ondo

APC, PDP, da Sauransu: Abubuwa 8 da Ya Kamata Ku Sani game da Siyasar Jihar Ondo

  • Jihar Ondo tana da tasiri mai girma a siyasar Najeriya, inda jam’iyyun PDP da APC suka fi daukar hankali a zaben da za a yi
  • Ondo ta fuskanci canje-canje na siyasa, inda manyan mutane kamar Olusegun Mimiko da Olusegun Agagu ke taka rawa
  • A yayin da za a gudanar da zaben jihar ranar Asabar, Legit Hausa ta lalubo wasu muhimman abubuwa game da siyasar Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - A ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne al’ummar Ondo za su fita rumfunan zabe domin zaben sabon gwamnan jiharsu kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna.

Masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa daya daga cikin 'yan takarar jam’iyyun PDP, APC, LP da kuma SDP ne zai iya lashe zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Hankalin PDP ya tashi, ƴan takarar gwamnan Ondo 3 sun janye, sun marawa APC baya

Cikakken bayani game da yanayin siyasar siyar jihar Ondo
Abubuwa 8 game da tsarin siyasar jihar Ondo. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

A yayin da ya rage saura awanni a gudanar da zaben, akwai wasu bayanan siyasa game da jihar Ondo da ya kamata ku sani:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Tarihin siyasar jihar Ondo

Jihar Ondo, wadda aka kafa a 1976, tana da tasiri sosai a fagen siyasar Kudu maso Gabashin Najeriya, dalilin da ya sa siyasar jihar ke da zafi.

A tsawon shekaru, jihar ta kasance karkashin 'yan siyasar da suka fito daga jam'iyyar PDP da APC, ko a wannan zaben na 2024, jam'iyyun ne a kan gaba.

Fitowar sababbin jam'iyyun siyasa, da suka fara karfi, irin su SDP, LP, ADC da sauransu ya kara canza yanayin siyasar jihar, duk da cewa wasu jam'iyyun sun janye daga zaben na bana.

2. Gasa tsakanin PDP da APC

Akwai tsananin hamayyar siyasa tsakanin PDP da APC a jihar Ondo, domin kowaccee jam'iyya na ganin za ta iya lallasa abokiyar karawarta.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 game da zaben gwamnan jihar Ondo

Duk da cewa APC ce ke mulki a jihar a yanzu, amma hakan bai hana PDP nuna karfin ikonta ba da kuma zama barazana ga jam'iyyar mai mulkin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa kananun jam'iyyun siyasa da ke tasowa, na iya zama hanyar rarrabewar kuri'un jama'a, amma duk da hakan, APC da PDP za su fafata sosai.

3. Manyan 'yan siyasa a jihar Ondo

Ondo ta samar da manyan 'yan siyasa da suka taka rawa a siyasar jihar da ma kasa baki.

Gwamnoni na baya kamar Dakta Olusegun Agagu (2003-2009) da Olusegun Mimiko (2009-2017) sun kasance manyan ginshikan siyasar jihar.

Vanguard ta rahoto wani dan majalisar tarayya, Abiola Makinde yana yabawa Mimiko kan irin gudunmawar da ya bayar a ci gaban jihar Ondo.

Ana ganin wadannan 'yan siyasar suna da tasiri mai yawa a jihar, wanda maganganunsu ko kuma goyon bayansu ga wani dan takara ka iya ba shi nasara.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jerin jihohin da jam'iyyun APC da PDP ke mulki yau a Najeriya

4. Yarbawa na taka rawa a siyasar Ondo

Kabilar Yarbawa da ita ce mafi rinjaye a jihar Ondo, tana taka muhimmiyar rawa a tsarin siyasar jihar a cewar rahoton WikiPedia

Tasirin al'adu da tarihi na wannan kabila ya zarce iya jihar Ondo inda ya kewaye dukkanin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

A matsayin daya daga cikin manyan kabilu a Najeriya, ra'ayoyin siyasa da alakar su suna shafar sakamakon zabe sosai.

5. Zaben gwamnoni da tsarin mika mulki

Ana tafka siyasa mai zafi a duk lokacin da zaben gwamnan jihar Ondo ya zagayo, musamman tsakanin manyan jam'iyyun siyasa a cewar rahoton This Day.

Domin dorewar dimokuradiyya, ba a samun wani kalubale na mika mulki a duk lokacin da aka samu canjin gwamnati.

Duk da hayaniyar zabe, ana ci gaba da gudanar da siyasar Ondo cikin kwanciyar hankali, kuma ana ganin sauye sauye a kowanne zagaye na zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Abubuwan sani dangane da Sola Ebiseni, dan takarar LP

6. Kalubale a tsarin siyasar jihar Ondo

The Punch ta rahoto cewa tsarin siyasa a jihar Ondo ba ya rasa kalubale. Tashe-tashen hankula a yayin zabe na ci gaba da ci wa hukumar INEC tuwo a kwarya.

Rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun siyasa na haifar da tashin hankula, inda wasu lokutan abin kan hada da hare haren 'yan ta'adda.

Har ila yau, matsaloli kamar cin hanci da rashawa, rashin aikin yi, da rashin kyakkyawar cibiyar gine-gine na ci gaba na shafar gudanar da zaben jihar.

Sai dai an ce shugabannin jihar sun dukufa wajen ganin an magance wadannan kalubale tare da tunanin gudanar da siyasa ba da gaba ba.

7. Tsarin siyasar Ondo da ingancin zabe

Tsarin siyasa na jihar Ondo yana aiki ne a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ke ba da dama ga jam'iyyun siyasa su nemi shugabanci.

Zabe a jihar yana gudana ne karkashin hukumar zabe ta kasa (INEC), wacce ke tabbatar da ingancin tsari da kuma gudanar da sahihin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Ana dab da fara zabe, 'yan daba sun farmaki 'yan PDP

Sai dai, akwai wasu lokuta da ake zargin cin hanci a zaben, musamman sayen kuri'u a lokacin da ake gudanar da zaben.

8. Yunkurin kawo tsaro da kwanciyar hankali

Jihar Ondo ta fuskanci matsaloli na rashin tsaro, musamman saboda ayyukan kungiyoyin 'yan dabar zabe da ma 'yan bindiga a yayin zabe.

A wannan karon, rundunar soji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun dauki matakan jibge jami'ansu domin tabbatar da an yi zaben cikin lumana.

Kungiyoyi, jam'iyyun siyasa da ma masu ruwa da tsaki sun yi ta kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da cewa ba a lalata sahihancin zaben jihar ba.

Ondo: 'Yan daba sun farmaki 'yan PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'Yan daba dauke da makamai sun farmaki 'yan jam'iyyar PDP yayin da suke gudanar da wani taro a Ondo.

An ce mutane kusan shida ne suka samu raunuka sakamakon farmakin, wanda ke zuwa awanni gabanin gudanar da zaben gwamnan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.