Ondo 2024: Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Ɗan Takarar Gwamnan SDP

Ondo 2024: Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Ɗan Takarar Gwamnan SDP

  • Otunba Bamidele Akingboye na jam'iyyar SDP na ɗaya daga cikin ƴan takara na sahun gaba da ake ganin za su iya kai labari
  • Hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamna a Ondo ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024
  • Legit Hausa ta binciko maku abubuwan da ya kamata ku sani game da ɗan takarar SDP, kwararre a fannin hada-hadar kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Otunba Bamidele Akingboye, ɗan kasuwa ne da ya yi fice a duniya, yana da gogewa a ɓangarori da dama kuma mutum ne mai taimakon jama'a.

Jam'iyyar adawa ta SDP ta ɗauko shi da ba shi tikitin takarar gwamna a zaben gwamnan Ondo da za a yi ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Otunba Akingboye.
Muhimman abubuwan sani game da ɗan takarar SDP a zaben gwamnan jihar Ondo Hoto: Otunba Akingboye
Asali: Facebook

Abubuwan sani kan ɗan takarar SDP

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Muhimman abubuwa dangane da 'yan takara 4 a APC, PDP, SDP da LP

Ɗan siyasar ya ce zai yi amfani da kwarewarsa wajen samar da damarmaki da wadata ga al'ummar Ondo idan suka amince suka zaɓe shi, Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana ɗaya daga cikin manyan ƴan takara a tsagin adawa waɗanda za su gwabza da Gwamna Lucky Auyedatiwa na jam'iyyar APC a zaben da za a yi.

Saboda haka ne Legit Hausa ta tattaro maku muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da Otunba Akingboye.

1. Daga wane yanki Akingboye ya fito?

A rahoton Dubawa, Akingboye ya fito ne daga Okitipupa, wani fitaccen gari a Ondo ta Kudu kuma hedkwatar karamar hukumar Okitipupa.

Galibin mazauna ƙaramar hukumar Okitipupa a jihar Ondo suna magana ne da yaren Ikale.

2. Nasarorin da ya samu a harkar kasuwanci

Kasancewarsa fitaccen ɗan kasuwa ba a Najeriya kaɗai ba har a ƙasashen duniya, Akingboye ya jagoranci harkokin kasuwanci da dama kuma ya ci nasara.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Cikakken jerin 'yan takarar gwamna a APC, PDP da sauran jam'iyyu

Ya jagoranci kamfanoni daban-daban da suka kunshi Benshore Maritime Services, Clog Oil Systems Ltd, Ben Bamigboye & Associates Ltd, Daily Best Industries Ltd, Fire Bee Services Ltd da sauransu.

"Ni ɗan kasuwa ne, na san yadda ake neman kudi kuma ina da gogewar jagorancin al'umma," in ji shi.

3. Yadda ya samu karɓuwa a duniya

Majalisar dinkin dunuya ta san da zaman Akingboye, ta ba shi matsayin jakadan zaman lafiya na UN.

Wannan ya ƙara tabbatar da kudirinsa na samar da ci gaba da zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin al'umma.

Har ila yau yana ɗaya daga cikin ƴan kungiyar kasuwanci ta Houston a Texas na ƙasar Anurka, sanann mamba ne a kungiyar Petroleum Club duk a Houston.

4. Karatun Otunba Akingboye na SDP

Ya yi karatu a makarantun Lagos Business School (da ta koma jami'ar Pan-Atlantic a yanzu), jami'ar Heriot-Watt da ke kasar Scotland da Harvard Business School.

Kara karanta wannan

Ondo: Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani kan Gwamna Aiyedatiwa da Ya Lashe Zabe

Akingboye ya yi alkawarin mayar da jihar Ondo ta zama cibiyar kirkire-kirkire da kere-kere, ta hanyar amfani da dimbin iliminsa da kwarewarsa ta duniya.

5. Shaidar karatu da kwarewa

Yana ɗaya daga cikin ƴan kungiyar masana harkokin kudi a Burtaniya kuma yana da satifiket na kwarewa wajen gano ƴan zamba da damfara.

Ɗan kasuwar yana da ƙarin takardun shaida na ƙwarewa a harkar haɗa rahoton kudi watau CertFR, sake fasalin kamfanoni da ƙungiyar kididdiga ta duniya, Cert IFR.

Bugu da ƙari, Akingboye na da shaidar karatun Diploma a fannin Akanta da kasuwanci, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

6. Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP

Ya kasance dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a 2003 sannan kuma ya yi takara a karkashin jam’iyyar DPP duk a jihar Ondo.

Otunba Akingboye ya zama ɗan takarar SDP a zaben Ondo 2024 bayan cika duk wasu tanade-tanaden dokokin zaɓe da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Abubuwan sani dangane da Sola Ebiseni, dan takarar LP

7. Manufar Akingboye a jihar Ondo

Otunba Akingboye ya kudiri aniyar mai da hankali wajen samar da arziki, inganta ababen more rayuwa, da bunkasa sabbin abubuwa idan ya zama gwamnan Ondo.

Gogewarsa a kasuwanci da fasaha da kuma kasancewarsa jakadan zaman lafiya ya sa ake ganin yana da cikin ƴan takarar da za su iya kai labari, rahoton Bussiness Day.

Gwamnonin da suka mulki Ondo daga 1999

A wani rahoton, mun kawo maku cikakken jerin gwamnonin da suka mulki jihar Ondo tun daga 1999 zuwa yau.

Jihar da ake yi wa lakabi da 'Sunshine state' ta samu gwamnoni akalla 19 da suka mulke ta da suka hada da sojoji da kuma na farar hula tun farkon kafa ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262