Zaben Gwamna: Kashim Shettima Ya Fadi Dalilan da za Su sa a Ƙara Zaben APC a Ondo

Zaben Gwamna: Kashim Shettima Ya Fadi Dalilan da za Su sa a Ƙara Zaben APC a Ondo

  • Jam'iyyar APC ta gudanar da gagarumin yakin neman zabe a birnin Akure na jihar Ondo yayin da ake shirin yin zaben gwamna
  • Tawaga mai karfi karkashin Sanata Kashim Shettima ne ta jagoranci yakin neman zaben inda yan APC suka nemi a zabe su
  • Mataimakin shugaban kasa ya bayyana wasu manyan dalilan da za su sanya mutanen Ondo su sake zaben APC a ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Jiga jigan APC sun dura jihar Ondo yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar mai zuwa.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bukaci mutanen Ondo su zabi APC saboda cigaba da Bola Tinubu ya kawo musu.

Zaben Ondo
APC ta yi yakin neman zaben karshe a Edo. Hoto: Ebenezer Adeniyan
Asali: Facebook

Legit ta samo bayanai kan yakin neman zaben ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan Ondo, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Jerin gwamnoni da suka mulki jihar daga 1999 zuwa yanzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga jigan jam'iyyar APC sun dura Ondo

Manyan jam'iyyar APC a Najeriya karkashin jagorancin Sanata Kashim Shettima sun je Ondo yi wa gwamna Lucky Aiyedatiwa yakin neman zabe.

A cikin tawagar akwai shugaban APC, Abdullahi Ganduje, gwamnan Legas, Sanata Barau Jibrin da kuma Sanata Adams Oshiomhole.

Haka kuma akwai ministan harkokin matasa, ministan tattalin arziki da sauransu.

Yakin neman zaben shi ne na karshe da APC ta shirya yayin da hukumar INEC za ta gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar.

Kashim Shettima ya bukaci a zabi APC

Mataimakin shugaban kasa ya buƙaci mutanen jihar Ondo su zabi dan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa.

Kashim Shettima ya ce Bola Ahmed Tinubu ya nuna dattaku wajen ba yan jihar Ondo muƙamai wanda hakan zai sa su kara zaben APC.

Ga dalilan da ya fada:

"Jihar Ondo tana da ministoci guda biyu kuma a makon da ya wuce shugaba Tinubu ya amince da kafa asibitin koyarwa a jami'ar FUTA.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Aiyedatiwa da wasu jerin ƴan takarar gwamna 3 da za su iya lashe zabe

Shugaban kasa ya yi haka ne domin nuna soyayya ga mutanen Ondo."

- Kashim Shettima

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa APC za ta lashe zabe a dukkan kananan hukumomin jihar 18.

PDP ta yi zargin shirin maguɗi a zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Ondo ta yi zargin cewa APC ta shirya maguɗi a zaben da za a yi kwanan nan.

Sakataren yada labaran PDP, Kennedy Peretei ne ya yi zargin inda ya ce an saka yan APC cikin wadanda za su yi aikin zabe a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng