Barau: Adam A. Zango Ya Shiga Tafiyar Kifar da Abba a 2027 a jihar Kano
- Shahararren dan wasan Kannywood, Adam A. Zango ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa Sanata Barau Jibrin ya karbi Adam Zango a gidansa na birnin tarayya tare da wasu abokan aikinsa
- Zango da ya yi fice sosai ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan Sanata Barau Jibrin lura da ayyukan alheri da ya ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tafiyar Sanata Barau I. Jibrin ta kara samun ƙarfi yayin da ya samu goyon bayan Adam A Zango.
Mawaki kuma dan wasan Kannywood, Adam A Zango ya yi wa Sanata Barau Jibrin kyauta ta musamman.
Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adam Zango ya shiga tafiyar Barau
Shahararren dan wasan Kannywood, Adam A Zango ya shiga tafiyar nuna goyon bayan ga Sanata Barau Jibrin.
Ana zargin mataimakin shugaban majalisar dattawan na cikin manyan yan APC da ke son kwace mulki a hannun NNPP a jihar Kano.
A karkashin haka, Adam Zango ya bayyana cewa zai cigaba da goyon bayan tafiyar Barau Jibrin da baiwar da Allah ya yi masa.
Dalilin shigan A. Zango tafiyar Barau
Adam A Zango ya bayyana cewa ya shiga tafiyar Sanata Barau Jibrin ne bisa yadda yake kokarin kawo cigaba ga al'umma.
Mawakin ya ce idan aka lura da ƙoƙarin da Sanata Barau ke yi, ya kamata kowa ya goyi bayansa.
Adam Zango ya ba Barau kyauta
A yayin ziyarar, Adam A Zango da wasu abokan aikinsa sun yi kyautar huluna da rigunan wasan kwaikwayo ga Sanata Barau Jibrin.
Barau Jibrin ya mika godiya ga Adam A. Zango tare da tabbatar da cewa zai cigaba da biyan bukatun al'umma.
Sanatan Kano zai yi karar shugaban NNPP
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Kawu Sumaila ya yi barazanar kai ƙarar shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa gaban kotu kan zargin ƙagen da ya masa.
A wata wasika da lauyan sanatan ya aike wa Hashimu, ya bukaci ya fito bainar jama'a ya janye kalamansa kuma ya ba da hakuri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng