Ondo: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna Kwanaki 2 gabanin Zaɓe

Ondo: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna Kwanaki 2 gabanin Zaɓe

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta sauke Olusola Ebiseni daga matsayin ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar LP a zaben da za ayi a Ondo
  • A zaman kotun na ranar Laraba, ta bayyana cewa ta gamsu da korafin LP da ta shigar da ƙara, ta soke hukuncin babbar kotun tarayya
  • Wannan hukunci na zuwa ne kwanaki biyu kacal gabanin zaben gwamnan jihar Ondo wanda za a yi ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta soke takarar Olusola Ebiseni na jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan da ake shirin yi nan da kwanaki biyu a jihar Ondo.

Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Adebukola Banjoko ne ya yanke hukuncin a ƙara mai lamba CA/ABJ/CV/1172/2024 da jam'iyyar LP ta shigar.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Hukumar zaɓe INEC ta canza ɗan takarar gwamna ana gobe zaɓe

Olusola Ebiseni.
Kotu ta kori ɗan takarar gwamnan Labour Party a zaben jihar Ondo Hoto: Olusola Ebiseni
Asali: Twitter

Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da bukatar LP

Kotun ta bayyana cewa ta amince da ƙorafin da jam'iyyar LP ta gabatar kan ɗan takarar gwamna, Cif Olusola Ebiseni da wasu mutum biyu, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, Mai Shari'a Banjoko, wanda ya karanto hukuncin ya ce nan ba da jimawa kotun za ta ba kowane ɓangaren takardar hukuncin da ta yanke.

A baya dai Mai Shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya ya umarci hukumar zaɓe INEC ta karɓi sunayen Olusola Ebiseni da Ezekiel Awude a matsayin ƴan takarar gwamna da mataimaki na LP.

Yadda ɗan takarar gwamnan ya samu tikitin LP

Mai shari’a Nwite ya gamsu da cewa zaben fitar da gwani na biyu da LP ta gudanar shi ne na gaskiya kuma shi ya kamata INEC ta amince da shi.

Alkalin ya aminta da hujjojin da ke nuna cewa Ebiseni ya biya Naira miliyan 20 na tsayawa takara kuma an ba shi fom kuma daga bisani aka shirya zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

Lagbaja: A ƙarshe, an birne gawar marigayi tsohon hafsan sojoji a Abuja

Don haka Nwite ya umarci INEC da ta amince da Ebiseni da Awude tare da buga sunayensu a matsayin halastattun ‘yan takarar LP a zaben gwamnan Ondo da za a yi ranar 16 ga Nuwamba.

Sai dai a yanzu kuma kotun daukaka kara ta soke wannan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, kamar yadda TVC News ta kawo.

Ondo: PDP ta zargi APC da shirin maguɗi

A wani rahoton, an ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Ondo ta yi zargin cewa APC ta haɗa kai da hukumar zabe ta kasa (INEC) domin mata murdiya.

Sakataren yada labaran PDP, Kennedy Peretei ya yi zargin cewa akwai wani makirci da APC ta kulla domin yin maguɗi a zaben gwamnan Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262