Farfesa Jega Ya Tona Asirin Yan Majalisar Tarayya, Ya Fadi Faman da Ya Yi da Su a INEC
- Tsohon shugaban hukumar INEC a Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya koka kan halayen wasu yan Majalisar Tarayya
- Jega ya bayyana yadda ya sha fama da su lokacin yana shugabantar hukumar INEC idan aka zo batun kasafi da kwangila
- Farfesan ya ce mafi yawan yan Majalisa na tilastawa masu rike da mukamai wurin tabbatar da karkatar da kasafinsu ko kwangila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega ya magantu kan yadda cin hanci ya yi kamari.
Farfesa Jega ya bayyana yadda wasu yan Majalisar Tarayya ke neman cushe a kasafin kudi domin biyan buƙatar kansu.
Jega ya jefi wasu 'yan Majalisar Tarayya da zargi
Jega ya fadi haka ne a yau Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024 a taron da hukumar ICPC ta shirya a Abuja, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Jega ya koka kan yadda yan Majalisar ke tilastawa masu rike da mukamai su biya musu bukatunsu.
Farfesan ya ce babban abin da ke hana Najeriya cigaba shi ne cin hanci inda ya koka kan yadda masu mukamai ke tsaka mai wuya daga yan Majalisa.
Maganar Farfesa Attahiru Jega
"Watakila akwai yan Majalisa a nan, amma zan yi magana, suna tilastawa masu rike da mukamai wurin bin abin da suke so ko da kuwa nagari ne."
"Yana da muhimmanci mutum ya kaucewa irin wadannan amma fa hakan yana da matukar wahala dai mutum ya dage."
- Attahiru Jega
Jega ya fadi wahalar da ya sha a INEC
Farfesa Jega ya tuno lokacin da yake hukumar INEC da irin matsin lamba da yake sha daga gare su.
Jega ya ce mafi yawansu suna matsa masa kan kasafin hukumar da kuma kwangiloli.
Jega ya gargadi masu fita kasashen ketare
Kun ji cewa tsohon shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shawarci yan Najeriya da su dai na ficewa daga kasar Farfesa.
Jega ya ce fita kasar waje neman mafita ba shi ne maganin wahalar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin Najeriya ba.
Ya shawarci jama’a kan matakan da ya dace su dauka wajen gina kasarsu, ba wai a bar ta zuwa kasashen da su ka gina kansu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng