Gwamna Ya Kori Hadimai da Shugabannin Hukumomi, Ya Umarci Kowa Ya Bar Ofis
- Gwamna Monday Okpebholo ya kori dukkan shugabannin hukumomi da masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar Edo
- Ya ɗauki wannan mataki ne sa'o'i 24 bayan karɓar rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar Edo
- Gwamnan ya kuma dakatar da tattara kuɗin shiga musamman a tasoshin mota, ya ce nan gaba kaɗan zai sanar da sabon tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Sabon gwamnan Edo da aka rantsar, Sanata Sunday Okpebholo ya sanar da rusa dukkan majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati a jihar.
Gwamnan wanda ya karɓi mulki daga hannun Godwin Obaseki, ya kuma kori dukkan hadiman da tsohon gwamnan ya naɗa kafin ya sauka.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan Edo, Fred Itua ya fitar yau Laraba, 13 ga watan Nuwamba, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya kori shugabannin hukumomi a Edo
Ya ƙara da cewa Gwamna Okoebholo ya kuma sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun da aka naɗa waɗanda ba ma'aikatan gwamnati ba.
"Ina sanar da al'umma cewa mai girma Gwamna Monday Okpebholo ya amince da korar shugabannin hukumomi da majalisun gudanarwa nan take.
"Bugu da ƙari, gwamnan ya kori dukkan manyan sakatarorin da aka ɗauko daga wajen hukumar ma'aikata tare da masu riƙe da nuƙaman siyasa."
"Don haka duk wadanda matakin ya shafa su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga babban jami’in gwamnati a ma’aikatu da hukumominsu.”
- Fred Itua.
Gwamna Okpebholo ya dakatar da tara haraji
Gwamna Okpebholo ya bayar da umarnin dakatar da tattara duk wasu kudin shiga na jihar, musamman a tashoshin mota da sauransu har sai wani lokaci.
Ya kuma umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo da ya kama duk wanda ya yi kunnen ƙashi, ya take umarnin, kamar yadda Punch ta kawo.
Gwamnan ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba, zai duba harkokin tattara kuɗin shiga sannan ya ɗauki matakin da ya dace.
Gwamnan Edo ya yi sababbin naɗe-naɗe
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya naɗa sakataren gwamnatin jihar Edo da kwamishinoni biyu awanni bayan karɓar mulki.
Ɗan tsohon shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole na cikin waɗanda sabon gwamnan ya ba muƙami a tashin farko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng