Gwamna Ya Nada Sabon SSG, Ya Ba Ɗan Tsohon Shugaban APC Babban Muƙami
- Gwamna Monday Okpebholo ya naɗa sakataren gwamnatin jihar Edo da kwamishinoni biyu awanni bayan karɓar mulki
- Ɗan tsohon shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole na cikin waɗanda sabon gwamnan ya ba muƙami a tashin farko
- A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, ya ce naɗin zai fara aiki ne bayan majalisar dokokin Edo ta tantance tare da tabbatar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Sabon gwamnan Edo da aka rantsar, Sanata Monday Okpebolo, ya nada Barista Musa Ikhilor a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SGG).
Wannan nadin tare da wasu shi ne na farko da gwamnan ya yi sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba.
Gwamma ya naɗa ɗan tsohon shugaban APC
Leadership ta ce gwamnan ya zabi tsohon dan majalisar tarayya, Dr Samson Osagie a matsayin Antoni-Janar na jihar kuma kwamishinan shari’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika Okpebholo ya amince da naɗin Dr. Cyril Oshiomhole a matsayin sabon kwamishinan harkokin lafiya.
Dr Cyril ya kasance ɗan tsohon gwamna kuma tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole wanda a yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa a majalisar dattawa.
Sababbin naɗe-naɗen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai (CPS) na gwamnan, Fred Itua ya fitar a yau Talata.
Gwamna Okpebholo ya miƙa sunayen majalisa
Ya ce naɗin zai fara aike ne da zaran majalisar dokokin jihar Edo ta tantance su idan Gwamna Okpebholo ya miƙa sunayensu, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Dr. Samson Osagie, wanda aka zaba a ofishin Akanta-Janar, lauya ne mai zaman kansa wanda ya fara aiki a matsayin cikakken lauya a Najeriya a ranar 22 ga Maris, 1995.
Har ila yau shi ne mataimakin shugaban kungiyar lauyoyin Afirka (yankin yammacin Afirka).
An haife shi a ranar 11 ga Nuwamba, 1967, kuma ya fito ne daga karamar hukumar Uhunmwode ta jihar Edo.
Tsohon gwamna na zargin EFCC da shirin kama shi
Ku na da labarin, gwamnan Edo da ya sauka, Godwin Obaseki ya yi zargin cewa EFCC na shirin cafke shi bayan ya miƙa mulki ga sabon gwamna.
Godwin Obaseki ya ce a bayanan da ya samu, EFCC na shirin cafke shi kan zargin zamba da karkatar da kudin talakawa a zamanin mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng