Gwamna a Arewa Ya Dawo da Kwamishinan da Ƴa Dakatar, An Samu Bayanai

Gwamna a Arewa Ya Dawo da Kwamishinan da Ƴa Dakatar, An Samu Bayanai

  • Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya maido da Antoni-Janar, Fidelis Mnyim bakin aiki bayan dakatar da shi a watan jiya
  • Sakataren watsa labaran gwamna, Tersoo Kula ya ce an dawo da shi ne bayan ya cika wasu sharuɗda da aka gindaya masa
  • A watan Oktoba, Alia ya dakatar da AG kuma kwamishinan shari'a saboda shigar da Benue cikin masu kalubalantar EFCC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na Benuwai ya ɗage dakatarwar da ya yi wa Akanta Janar (AG) kuma kwamishinan shari’a, Mista Fidelis Mnyim.

Gwamna Alia ya sanar da mayar da shi bakin aiki ne a ranar Litinin a Makurdi yayin taron majalisar zartarwa ta jiha (SEN) wanda ya jagoranta.

Gwamma Alia.
Gwamna Alia ya maido kwamishinan shari'a kan aikinsa Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan Benue ya dakatar da kwamishinan shari'a daga aiki ne a ranar 23 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Amorim: Sabon kocin Manchester United ya kama aiki, an sallami mutum 4 daga kulob

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya dakatar da kwamishinan shari'a

Alia ya dakatar da shi ne a lokacin da ya sanya jihar Benuwai a jerin jihohin da suke kalubalantar halascin kafa hukumomin cin hanci, EFCC da ICPC.

Babban sakataren watsa labaran gwamnan Benuwai, Sir Tersoo Kula, ya tabbatar da maido da kwamishinan da yake hira da manema labarai a yau Litinin.

Mista Kula ya ce gwamna ya amince da dawo da Mnyim bayan ya cika sharuɗɗa ciki har da zare jihar Benuwai daga jihohin da suke kalubalantar kafa EFCC.

Ya ce kwamishinan shari'an ya cika dukkan sharuɗɗan da Mai girma gwamna ya gindiya masa kafin a dawo da shi bakin aiki.

Gwamnatin Benue za ta gina tituna

Bugu da ƙari, majalisar zartawan Benuwai ta amince da ware N30.2bn domin gina wasu tituna a faɗin mazaɓun sanatoci uku.

Hanyoyin da za a gina su ne Awajir/Oju, Adikpo/Kotiyo/Vandeikya, Ushongo/Har, Igwumale/Agila da kuma titin Obagaji/Okokolo/Agagbe.

Kara karanta wannan

Dan NNPP ya saɓawa gwamnonin Arewa, zai marawa kudurin haraji baya a majalisa

Gwamna Alia ya naɗa sabuwar SSG

A wani rahoton, an ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya naɗa Barista Aber Deborah a matsayin sabuwar sakatariyar gwamnatin jiha (SSG).

Alia ya yi wannan sanaɗi ne bayan Farfesa Joseph Alakali ya yi murabus daga kujerar SSG saboda wasu dalilai na ƙashin kansa.

Muhammad Malumfashi, babban Edita na sashen Hausa, Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262