Tinubu Ya Faɗi Jihar da Yake So APC Ta Kwace a Zaben 2027, Ya Ce Tana da Muhimmanci

Tinubu Ya Faɗi Jihar da Yake So APC Ta Kwace a Zaben 2027, Ya Ce Tana da Muhimmanci

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugabannin APC na Oyo su jingine saɓani, su kwato mulkin jihar daga hannun PDP a 2027
  • Shugaban ƙasar ya ce jihar Oyo na da matuƙar muhimmanci don haka bai kamata a ce ba ta cikin jerin jihohin da APC ke mulki ba
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a taron da ya wakilci Bola Tinubu a Ibadan ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci jagororin APC da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar Oyo su jingine saɓanin da ke tsakaninsu.

Shugaba Tinubu ya roki masu ruwa da tsakin APC reshen Oyo su yi duk mai yiwuwa, su manta da saɓani su kwato mulkin jihar a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya buƙaci shugabannin APC su kwato jihar Oyo a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yi wannan roko ne a taron lakcar tunawa da marigayi tsohon gwamnan Oyo, Lam Adesina a Ibadan, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya buƙaci APC ta karɓe mulkin Oyo

Shugaban ƙasar wanda ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya wakilta, ya ce jihar Oyo na da matuƙar muhimmanci, bai kamata a ce ba ta hannun jam'iyyar APC ba.

Ya kuma ce marigayi Adesina gwarzo ne, wanda ya rubuta sunansa a jerin mutanen da Najeriya ke alfahari da su saboda jarumta da jajircewarsa.

Shugaba Tinubu ya ce:

"Adesina ya tsaya kan kyawawan manufofin tsarin demokuraɗiyya, ya ba da gudummuwa wajen kafuwarta tare da tabbatar da al'umma na da ta cewa a harkokin mulki."

Marigayi Adesina ya yi mulki a jihar Oyo daga 1999 zuwa 2003 kuma Allah ya masa rasuwa a sheksrar 2012.

Manyan jiga-jigan da suka halarci taron a Ibadan

Manyan jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da tsofaffin gwamnonin Ekiti, Adeniyi Adebayo da Kayode Fayemi.

Kara karanta wannan

'Ku tsaya gida, ku bar fita kasar waje,' Tinubu ya aika sako ga matasa masu digiri

A ciki akwai tsohon sanata kuma dan takarar gwamna na APC a zaben 2023 a Oyo, Teslim Folarin da Sanata Abdulfatai Buhari.

Sai tsohon mataimakin gwamnan jihar, Iyiola Oladokun, Alake Adeyemo, mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na Oyo, Olayide Abas, Femi Lanlehin da sauransu.

Jam'iyyar APC ta maida martani ga Atiku

Mun kawo rahoton, APC mai mulki ta yi martani kan yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ke cigaba da sukar gwamnatin Bola Tinubu

APC ta ce bai kamata a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa ya rika sukar gwamnati a kai a kai ba maimakon zamowa dattijon ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262