Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar NNPP Ta Sake Taso Kwankwasiyya a Gaba
- Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na tsagin jam'iyyar NNPP ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
- NWC ya nuna yatsa ga Kwankwaso ne bisa ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Abia, Alex Otti
- Kwamitin na NWC ya bayyana ziyarar a matsayin wani shiri na yaudara da Kwankwaso ke yi na haifar da rikici a jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na tsagin jam’iyyar NNPP, ya yi Allah-wadai da ziyarar da tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai wa Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
A wani taron gaggawa da aka yi a Otal ɗin Rockview, Apapa, Legas, NWC ya bayyana ziyarar Kwankwaso a matsayin "shirin yaudara" da ke da alaƙa da hukuncin kotu kan rikicin cikin gida na jam'iyyar.
NNPP ta caccaki Kwankwaso da Kwankwasiyya
NNPP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta, Abdulrasalam Abdulrazaq, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin NNPP dai ya ƙara ƙamari ne bayan wani tsagin jam'iyyar ya kori Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƴan ƙungiyar Kwankwasiyya.
Jam’iyyar ta bayyana cewa an kori Kwankwaso da ƴan ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya daga NNPP, kuma duk wani yunƙurinsu na wakiltar kwamitin zartaswa aiki ne na rashin kirki da yin sojan gona.
Har ila yau, NWC ya nuna cewa waɗanda aka kora ba su da wani muƙami da aka sani a cikin jam’iyyar NNPP, kuma iƙirarin da suke yi na cewa su shugabanni ne ba shi da inganci.
Jam'iyyar NNPP ta ba gwamnan Abia shawara
NWC ta buƙaci Gwamna Otti da ya kaucewa shiga harkokin cikin gida na jam’iyyar NNPP, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Hakazalika, ta soki Kwankwaso da kan zargin yin amfani da ƙarfin ikonsa wajen haifar da saɓani a cikin jam'iyyar NNPP tun bayan shigowarsa a shekarar 2022.
A cewar NWC, manufar Kwankwaso ita ce ta “ƙwace” jam’iyyar saboda amfanin kansa, don ya ci amanar waɗanda suka kafa ta.
NWC ta sake tabbatar da Boniface Aniebonam a matsayin shugaban kwamitin amintattu kuma wanda ya kafa jam'iyyar, inda ta haƙiƙance cewa an kori Kwankwaso da ƴan tawagarsa.
Kwanwaso ya taya Trump murnar cin zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, murnar nasarar da ya samu a zaɓe.
Saƙon taya murnar na Kwankwaso na zuwa ne bayan Donald Trump ya yi nasara kan Kamala Harris a zaɓen shugaban ƙasan Amurka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng