Tinubu Ya Fusata kan Wasu Kalaman Atiku, Ya yi Zazzafan Martani

Tinubu Ya Fusata kan Wasu Kalaman Atiku, Ya yi Zazzafan Martani

  • Fadar shugaban kasa ta yi zazzafan martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan sukan tsare tsaren Bola Tinubu
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ce Atiku Abubakar yana yi wa Bola Tinubu hassada ne tun bayan kayar da shi zabe da aka yi a shekarar 2023
  • Hakan na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya matsa lamba ga shugaba Bola Tinubu a kan yadda lamura ke tafiya a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi Allah wadai da kalaman da Atiku Abubakar ya yi a kan Bola Tinubu.

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce a yanzu haka tsare tsare da ta kawo sun fara ɗaukar hanyar daidaita Najeriya ba kamar yadda Atiku ke tunani ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Atiku
Fadar shugaban kasa ta bukaci Atiku ya fuskanci rikicin PDP. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Asali: Getty Images

Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya yi martani a madadin Bola Tinubu a wani sako da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ka fuskanci rikicin PDP' - Tinubu ga Atiku

Fadar shugaban kasa ta ce bai kamata Atiku Abubakar ya rika tsoma baki ga Tinubu a kan mulki ba alhali jam'iyyarsa na cikin rikici.

Ta bakin hadiminsa, Bola Tinubu ya ce ya kamata Atiku Abubakar ya magance matsalolin PDP a karon farko kafin maganar rikicin Najeriya.

Haka zalika ya kara da cewa duk wani dadin baki da Atiku zai yi, yan Najeriya ba za su manta da yadda PDP ta lalata Najeriya ba a shekaru 16 da ta yi.

Ko Atiku na yi wa Tinubu hassada?

Fadar shugaban kasa ta ce laifin Atiku ne ya jawo masa faduwa a zaben 2023 ba wai Bola Tinubu ne ya yi masa kwace ba kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargi.

Kara karanta wannan

An sake gabatar da bukatar maido tallafin man fetur ga Tinubu

A karkashin haka, fadar shugaban kasa ta ce a bisa dukkan alamu Atiku na yi wa Bola Tinubu hassada ne kan samun shugabanci da ya nema sau shida bai samu ba.

Maganar cire tallafin man fetur

Fadar shugaban kasa ta ce maganar da Atiku yake a kan cire tallafin man fetur ba za ta kai Najeriya tudun tsira ba.

A karkashin haka, gwamnatin Bola Tinubu ta buƙaci Atiku Abubakar ya yi jinjina ga shugaban kasa kan matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur.

APC ta yi kira ga Atiku Abubakar

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi martani kan yadda Atiku Abubakar ke cigaba da sukan gwamnatin Bola Tinubu.

APC ta ce bai kamata a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa ya rika sukan gwamnati a kai a kai ba maimakon zamowa dattijon ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng