'Kano ba Ta Kwankwasiyya ba ce kaɗai': Kawu Sumaila Ya Ja Kunnen Abba Kabir

'Kano ba Ta Kwankwasiyya ba ce kaɗai': Kawu Sumaila Ya Ja Kunnen Abba Kabir

  • Yayin da rigimar jam'iyyar NNPP ke kara ƙamari, Sanata Kawu Sumaila ya yi magana inda ya shawarci Gwamna Abba Kabir
  • Sanata Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya ce ya kamata Abba ya sani ba iya yan Kwankwasiyya ba ne kaɗai a jihar
  • Sumaila ya ce babban cin amana shi ne bijirewa Allah da ya yi masa gata a rayuwarsa inda ya ba shi shawara kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sanata Kawu Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya yi magana kan rigimar siyasa a jihar Kano.

Sumaila ya shawarci Gwamna Abba Kabir ya yi adalci ga dukkan yan jihar ba tare da nuna wariyar jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

'Akwai riba': Gwamna ya fadi yadda rikicin da ke faruwa a jiharsa ya zama alheri

Kawu Sumaila ya ba Abba Kabir shawara kan siyasar Kano
Sanata Kawu Sumaila ya ja kunnen Abba Kabir kan yiwa mutanen Kano adalci gaba daya. Hoto: Sen. S A Kawu Sumaila, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kawu Sumaila ya ba Abba Kabir shawara

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu ya fadi haka ne yayin ganawa da manema labarai inda ya ba Abba shawara kan Rabiu Kwankwaso, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sumaila ya ce ya kamata Abba Kabir ya mutunta Kwankwaso sai dai ya ce bai kamata ya fifita yan Kwankwasiyya ba.

"Mu na da mutane kusan miliyan 20 a Kano duk da Abba ya yi alkawari ba zai ci amanar Kwankwaso ba amma ya sani akwai al'umma da ke ƙarƙashinsa."
"Bai kamata su ma ya ci amanarsu ba saboda su suka zabe shi, mutane miliyan daya da kadan suka zabe shi wadanda suka wakilci sauran al'umma."
"Abin da nake so ya sani shi ne mafi munin cin amana shi ne bijirewa Allah wanda ya yi masa komai a rayuwarsa."

Kara karanta wannan

'Babu laifi': Lauyan Tinubu ya sake magana kan yaran da aka kama, ya fadi tsarin doka

- Kawu Sumaila

Kan rikicin NNPP, Kawu Sumaila ya ce ya ji dadin matakan da ake dauka wurin sasanta Abba Kabir da Kwankwaso inda ya shawarce shi kan sulhu da yan adawa.

Jiga-jigan NNPP sun koma APC a Kano

Kun ji cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano sun watsar da tafiyar Kwankwasiyya yayin da suka koma APC.

Jiga-jigan sun samu tarba wajen mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin bayan sun dawo APC.

Sanata Barau ya bayyana masu sauya sheƙar inda sun nuna gamsuwarsu kan irin ayyukan alherin da yake yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.