'An Rasa Inda Yake': An Zargi Gwamna da Tserewa daga Gidan Gwamnati Tun Juma'a
- Gwamna mai jiran gado, Sanata Monday Okpebholo ya yi zargin cewa ana neman Gwamna Godwin Obaseki an rasa
- Okpebholo ya ce tun ranar Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024 har zuwa yau ba a san inda Obaseki yake ba
- Hakan ya biyo bayan zargin da Obaseki ya yi na cewa Okpebholo bai gayyace shi zuwa taron rantsar da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi zargin APC taki gayyatarsa bikin mika mulki.
Gwamna mai jiran gado, Sanata Monday Okpebholo ya mayar masa da martani mai zafi kan zarge-zargen.
An zargi Obaseki da tserewa a gidan gwamnati
Vanguard ta ruwaito cewa Okpebholo ya ce tun ranar Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024 babu duriyar Gwamna Obaseki a Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okpebholo ya ce tun ranar Juma'a ba a sake jin duriyarsa ba kuma babu wanda ya yi magana da shi, cewar Daily Post.
A cikin wata sanarwa a yau Lahadi 10 ga watan Nuwambar 2024, Okpebholo ya ce yan jihar sun fara firgita kan kalaman Obaseki.
Sanata Okpebholo ya ce a yanzu Obaseki ya buge da furta wasu irin kalamai da ya cancanci a binciki lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
Ana zargin Obaseki ya kori kowa a gwamnati
"Tun ranar Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024, ba a san inda Gwamna Obaseki yake ba."
"Ya kori kowa a gidan gwamnati bayan shi ma ya tsere yanzu haka ba a san halin da yake ciki ba."
"Ya tsere daga Benin, idan har ya cika jarumi meyasa bai yi amfani da fasfo ba sai ya hau motar bas ya tsere?"
- Monday Okpebholo
Gwamna Obaseki ya yi garambawul a gwamnatinsa
Kun ji cewa kwanaki ƙadan kafin barin mulki, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai.
Obaseki ya dauki matakin ne yayin da yake kwanakin karshe na wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin rantsar da Sanata Monday Okpebholo na APC a matsayin sabon gwamna a ranar 12 ga watan Nuwambar 2024.
Asali: Legit.ng