Abinci Ya Kare: Gwamna Ya Rusa Dukan Masu Mukamai a Gwamnatinsa, Ya Yi Godiya
- Kwanaki ƙadan kafin barin mulki, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai
- Obaseki ya dauki matakin ne yayin da yake kwanakin karshe na wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Edo da ke Kudancin Najeriya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin rantsar da Sanata Monday Okpebholo na APC a matsayin sabon gwamna a ranar 12 ga watan Nuwambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya yi garambawul a gwamnatinsa ana saura kwanaki uku ya sauka.
Obaseki ya sallami dukan masu mukamai a gwamnatinsa yayin da ake shirin rantsar da gwamnatin APC.
Gwamna Obaseki ya godewa mukarrabansa a Edo
The Guardian ta ce Obaseki ya dauki matakin ne a jiya Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024 a birnin Benin City.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya godewa mukarraban nasa kan irin gudunmawar da suka ba shi tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki.
Obaseki ya shiga ofis ne a ranar 12 ga watan Nuwambar 2016 da ake tsammanin zai kammala wa'adinsa ranar 12 ga watan Nuwambar 2024, cewar Vanguard.
Mataimakin gwamnan, Godwins Omobayo shi ya kawo kudirin rusa masu rike da mukaman wanda ya samu goyon bayan kwamishinan Kasafi, Osilama Okuofu.
Daga bisani gwamnan ya kuma godewa al'ummar jihar kan irin addu'o'i da suka yi ta masa da kuma goyon bayansu tsawon shekaru.
Mukarraban Gwamna Obaseki sun yi masa godiya
A bangarensu, Majalisar zartarwa da sauran masu mukaman sun yabawa gwamna Obaseki kan damar da ya ba su.
Sun kuma yaba masa kan ayyukan alheri da ya yi a jihar da sauran cigaba a fadin Edo wanda ya zama daban da sauran gwamnoni.
Kano: Abba Kabir ya shirya yin garambawul
Mun baku labarin cewa Gwamna Abba Kabir ya shirya yin garambawul a gwamnatinsa nan ba da jimawa ba.
Gwamnan ya tabbatar da haka ne bayan karbar rahoto daga kwamiti na musamman kan ayyuka da ƙoƙarin kwamishinoni.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da zargin baraka tsakanin Abba da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso wanda ya musanta.
Asali: Legit.ng