Wasu Manyan Jiga Jigai da Dubannin 'Yan APC Sun Gaji da 'Wahala', Sun Koma PDP

Wasu Manyan Jiga Jigai da Dubannin 'Yan APC Sun Gaji da 'Wahala', Sun Koma PDP

  • Manyan kusoshi da dubannin ƴaƴan APC mai alamar tsintsiya, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun
  • A wata sanarwar haɗin guiwa da suka fitar, masu sauya sheƙar sun ce ba za su iya ci gaba da zama a jam'iyyar da ba ta damu da jama'a ba
  • Sun kuma tabbatar da cewa ƴaƴan APC na ci gaba da yin tururuwa zuwa PDP a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Wasu jagororin jam'iyyar APC da dubannin mambobi a ƙananan hukumomi 30 sun sauya sheƙa zuwa PDP mai mulki a jihar Ogun.

Ƴan siyasar sun bayyana cewa darewar APC zuwa tsagi-tsagi da wahalar da ake sha a ƙasa ne ya sa suka tattara kayansu suka sauya sheka.

Kara karanta wannan

Matasa sun taso da batun kuɗin NPower, sun aika muhimmin saƙo ga sabon minista

PDP da APC
Jam'iyyar PDP ta samu karuwa da dubbannin ƴan APC suka dawo cikinta a Osun Hoto: @OfficailPDPNig, OfficialAPCNG
Asali: Twitter

Rahoton Tribune ya ce hakan na ƙunshe ne a wata sanarwar haɗin guiwa da masu sauya shekar suka fitar ranar Juma'a ɗauke da sa hannun Hon. Oluomo Owolabi da wasu mutum 31.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin ƴan PDP sun yabawa Gwamna Adeleke

Tawagar masu sauya sheƙar sun kuma yabawa Gwamna Ademola Adeleke na PDP bisa sauye-sauyen da ya kawo tun da ya hau gadon mulki a jihar Edo.

Jagororin siyasar sun tabbatar da wani raɗe-raɗi da ake cewa kusan kaso 45% na ƴan tsagin tsohon gwamna a APC sun sauya sheƙa zuwa PDP.

A cewarsu, sun samu kyakkaywar tarba a PDP kuma a shirye suke su haɗa kai domin ɗaga martabar jihar Osun.

Dalilin jiga-jigan APC na komawa PDP a Osun

A wani sashin sanarwar, an ji jagororin masu sauya sheƙar na cewa:

"Mun bar APC saboda jam'iyyar ba ta da alƙibla, ta rasa ƙima, sannan ta jefa jama'a cikin ƙunci. Mun baro APC saboda mu zo mu ba da gudummuwa a gina jiharmu.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun samu babbar nasara, sun kashe ƴan bindiga sama da 400

"Muna jin daɗin yadda Gwamna Ademola Adeleke ya kawo sauyi, a baya APC ta gaza a Osun amma yanzu gwamnatin PDP ta zo da alheri ga jama'a, shiyasa muka shigo mu ba da gudummawa."

Tsohon ɗan majalisa ya rungumi APC

A wani rahoton kun ji cewa tsohon ɗan majalisar tarayya da ya wakilci mazaɓar Anka/Talata Mafara, Kabiru Classic ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kabiru Classic ya ɗauki wannan mataki ne bayan ganawa da shugaban APC na Zamfara da wasu manyan masu ruwa da tsaki a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262