APC Ta Yi Manyan Kamu, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

APC Ta Yi Manyan Kamu, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

  • Tsohon ɗan majalisar tarayya da ya wakilci mazaɓar Anka/Talata Mafara, Kabiru Classic ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Kabiru ya ɗauki wannan mataki ne bayan ganawa da shugaban APC na Zamfara da wasu manyan masu ruwa da tsaki a Kaduna
  • Ɗan siyasa kuma fitaccen mawakin ya sauya sheƙa tare da kusan dukkan shugabannin APC na ƙaramar hukumar Talata Mafara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Alhaji Kabiru Classic ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar Zamfara

Kabiru Classic ya sanar da sauya sheka ne a ranar Alhamis bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Tukur Danfulani da wasu jiga-jigai a Kaduna.

Kara karanta wannan

Hadimar Gwamna Abba kuma jarumar Kannywood ta fice daga NNPP zuwa APC

Kabiru Classic.
Zamfara: Tsohon ɗan majalisa ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Dan Bazuka
Asali: UGC

Channels tv ta ce waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da shugaban magoya bayan Sanata Abdul’aziz Yari, Alhaji Lawal M Liman da wasu masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ɗan majalisar ya ruguza jam'iyyar PDP

Alhaji Kabiru Yahaya Classic ya wakilci mazabar Anka/Talata Mafara a majalisa ta tara tsakanin 2019 zuwa 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Tsohon ɗan majalisar ya koma APC tare da shugabannin PDP na ƙaramar hukumar Talata Mafara ciki har da shugaban jam'iyyar.

Kabiru Classic ya bayyana cewa ya yanke shawarar tattara kayansa ya bar PDP ne saboda rashin adalcin da ake yi a jam'iyyar ta reshen Zamfara.

Jiga-jigan PDP sun koma APC a hukumance

"Ni Kabiru Yahaya Classic, a yau Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, 2024, ina sanar da cewa na fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC."
"Na taho da gaba ɗaya tsarin PDP na Talata Mafara ciki har da shugabannin jam'iyya na ƙaramar hukumar da 10 daga cikin ciyamomi 11 da muke da su a gundumomi."

Kara karanta wannan

Uwargidar shugaban ƙasa da wasu mata 2 sun dura gidan marigayi hafsan sojin ƙasa

- Kabiru Classic

APC ta yi murna da sauya shekar Kabiru

Da yake karbar tsohon dan majalisar, shugaban APC na Zamfara, Tukur Umar Danfulani ya bayyana sauya shekar Kabiru Classic a matsayin abin maraba.

Tribune ta rahoto shi yana cewa:

"Muna farin cikin karbar dan uwanmu zuwa inuwar jam'iyyarmu mai albarka, wannan babban ci gaba ne. Nan ba da jimawa wasu jiga-jigai daga gwamnatin Zamfara za su bar PDP."

Hadimar gwamnan Kano ta koma APC

A wani rahoton, an ji cewa jarumar Kannywood kuma mai taimakawa gwamnan Kano, Asma'u Abdullahi, ta fice dagaNNPP da Kwankwasiyya.

Barau Jibrin ya shaida cewa Asma'u Abdullahi ta tsallaka zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar bayan ta yi murabus daga muƙaminta a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262