'Za Mu Gyara Najeriya,' Bukola Saraki Ya Fadi Shirin da PDP Ta Yi na Karbar Mulki a 2027

'Za Mu Gyara Najeriya,' Bukola Saraki Ya Fadi Shirin da PDP Ta Yi na Karbar Mulki a 2027

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce PDP za ta yi duk mai yiwuwa domin gyara matsalolinta da na Najeriya
  • Makinde ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da kwamitin gwamnoni da sababbin manufofin cibiyar PDP ta PDI
  • A jawabinsa, Bukola Saraki ya bukaci a gina PDP tare da guje wa dogon buri, inda ya nuna tasirin hakan ga zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce jam'iyyar PDP za ta yi duk mai yiwuwa domin gyara matsalolinta da kuma gyara Najeriya.

Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin kaddamar da kwamitin gwamnoni da sababbin manufofin cibiyar PDP ta PDI.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa zai kashe N93bn a samar da ruwa, zai biya ma'aikata bashin N800m

Makinde, Saraki sun yi magana kan gyara PDP gabanin zaben 2027
Saraki, Makinde sun nemi a gina PDP domin karbar mulki daga APC a 2027. Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Gwamna ya fadi matakin nasarar jam'iyyar PDP

PDI ita ce cibiyar bincike ta PDP da aka kafa a shekarar 2000 domin inganta al'adun dimokiradiyya a Najeriya da Afirka, kamar yadda PM News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Makinde ya ce:

“Za mu gyara PDP, sannan PDP za ta gyara Najeriya. 'Yan Najeriya na kallon PDP a matsayin wanda za ta samar da jagoranci mai ma'ana."

Gwamnan na Oyo ya ce PDP na bukatar warware rikice-rikicenta da hadin kai a tsakanin 'ya'yanta domin kwace mulki daga jam'iyyar APC.

2027: Bukola Saraki ya nemi a gina PDP

A jawabinsa, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya jaddada bukatar gina PDP tare, yana mai cewa jam’iyyu su kan ginu ne bisa tunani, falsafa da manufofi.

Vanguard ta rahoto Sararki ya bukaci 'yan PDP su guji gina tunani kan buri kashin kai, yayin da Najeriya ke tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Ban tsoron EFCC': Gwamnan PDP ya bugi kirji, ya fadi abin da zai yi idan suka neme shi

“Akwai bukatar mu daina magana kan wanda zai tsaya takarar kansila, ko wanda zai tsaya takarar gwamna, ko wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
"Maimakon haka, mu tattauna me ya gina PDP, me PDP ke wakilta? Waɗannan su ne batutuwan da ya kamata mu yi la’akari da su gabanin 2027.”

- Bukola Saraki.

PDP za ta dauki daraktan cibiyar PDI

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta sanar da daukar ma’aikacin da zai mata aiki a matsayin Darakta Janar na cibiyar People Democratic Institute (PDI).

PDP ta ce dole ne wanda ke da sha’awar yin aikin ya zama yana da digiri na biyu a fannin ilimin zamantakewa kuma ya kasance kwararre mai gogewar aiki na akalla shekaru shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.