Kwanaki 9 Kafin Zaɓe, Kotu Ta Raba Gardama kan Sahihancin Dan Takarar NNPP
- Yayin da ake shari'a kan sahihancin dan takarar gwamna a NNPP, kotu ta raba gardama kan lamarin a Ondo
- Kotun ta yi fatali da masu kalubalantar takarar Olugbenga Edema kan zargin cewa ba dan jam'iyya ba ne tun farko
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Babbar Kotun jihar Ondo ta yi hukunci kan sahihancin dan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP.
Kotun ta yi fatali da korafe-korafen da aka shigar kan takarar Olugbenga Edema ana daf da gudanar da zaɓe.
Dan takarar NNPP ya yi nasara a kotu
Punch ta ce yayin hukuncin, an tabbatar da sahihancin takarar Edema a zaben gwamnam jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan shigar da korafi inda ake kalubalantar kasancewar Edema dan jam'iyyar NNPP.
Wanda ya yi takara a zaɓen fitar da gwani, Michael Akintan da Mrs Femi Fasua su suke kalubalantar Edema.
Suna korafi kan sahihancin Edema da kuma kasancewarsa asalin dan jam'iyyar a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Ondo: Edema ya kalubalanci korafi kan takararsa
Har ila yau, Edema da mataimakinsa a zaben, Rotimi Adeyemi sun bukaci kotu ta yi farali da korafe-korafen da aka shigar kansu.
Sun shigar da korafi ne ta bakin lauyansu, Rotimi Olunfemi inda ya ce ya kamata a shigar da korafin ne a gaban Babbar Kotun Tarayya, cewar The Guardian.
A martaninsa, Edema ya ce hukuncin ya tabbatar da ko shi cikakken dan jam'iyyar NNPP ne ko kuma sabanin haka.
Jigon APC ya sami takara a NNPP
A baya, kun ji cewa Barista Olugbenga Edema ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Ondo a inuwar NNPP bayan ya baro jam'iyyar APC.
Tsohon jigon jam'iyya mai mulki ya ce ya shirya sauke Gwamna Lucky Aiyedatiwa daga mulki a zaɓen watan Nuwamba, 2024.
NNPP ta ba Edema tikitin takara ne bayan tsohon ɗan takararta, Oluwatosin ya janye daga takara bisa ra'ayin kansa da kishin jam'iyya.
Asali: Legit.ng