Rikicin NNPP: Gwamna Abba Ya Ɗauki Zafi, Ya Yi Magana kan Daina Ɗaga Kiran Kwankwaso
- A karshe Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana gaskiya kan zargin da ake cewa ya fara samun matsala da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso
- Gwamna Abba ya ce jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya daina ɗaga kiran Kwankwaso ƙarya ne domin ba zai ci amanarsa ba
- Abba ya kuma ɗauki zafi kan ƴan jarida inda aka ji yana cewa ba don yana ganin girmansu da kotu za ta raba su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta zargin cewa alaƙarsa da ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso ta yi tsami har ya daina ɗaga wayarsa.
Gwamna Abba ya ce ba don yana ganin girman ƴan jarida ba da sai ya maka wanda ya yi wannan rubutun a kotu.
Abba ya faɗi haka ne a wata hira da ƴan jarida kan jita-jitar kuma mai magana da yawunsa, Sanusi Bature ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya musanta ƙin ɗaga kiran Kwankwaso
Wannan na zuwa ne yayin da ake yaɗa rahoton cewa alaƙar Abba da Kwankwaso ta yi tsami, har wasu na cewa ya daina ɗaga wayar jagoran jam'iyyar NNPP
Da yake martani gwamnan ya ce raɗe-raɗin da wasu masu neman tayar da fitina suke yaɗawa cewa Kwankwaso ya kira shi sau sama da 30 amma bai ɗaga ba ƙarya ne.
Abba Kabir ya ce kujerar gwamnan da yake kai Allah ne ya ba shi amma Kwankwaso ne sila, yana mai karawa da cewa ba a san kanawa da butulci ba.
"So ake na ci amanarsa" Gwamna Abba
"Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Wannan kujerar ta gwamna ya kamata jama'a su sani kanawa fa ba a sanmu a cin amana ba, Allah ne ya bani amma wannan mutumin (Kwankwaso) shi ne sila."
"So ake silar da Allah ya nufa na zama, shi zan shiga in ci wa mutunci? Har ana cewa wai ya kira ni sau 30 da kaza ban ɗauka ba, shin a ina suka samu wannan?"
"Kuma ni ba don ina girmama ƴan jarida ba kuma ina mu'amala da su wallahil Azeem sai na kai wanda ya yi wannan rubutun kotu, amma ni da mai girma jagora mun san ƙarya ne."
- Abba Kabir Yusuf.
A karshe gwamnan ya yi kira ga masoyansa a lungu da saƙo na ƙasar nan cewa ka da ya ƙata jin maganar 'Abba tsaya da ƙafarka'.
Majalisar Kano ta musanta rabuwa gida biyu
A wani rahoton, an ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Hussaini ya yi bayani kan zargin rabuwar kai a tsakanin yan NNPP.
Hon. Lawan Hussaini ya bayyana cewa har yanzu babu wata ɓaraka a tsakanin yan majalisun NNPP a majalisar dokokin jihar Kano.
Asali: Legit.ng