"Na Gamsu da Ayyukan da na Yi," Gwamna Ya Ce Ya Cika Alkawurran da Ya Ɗauka a Kamfe

"Na Gamsu da Ayyukan da na Yi," Gwamna Ya Ce Ya Cika Alkawurran da Ya Ɗauka a Kamfe

  • Gwamnan Edo mai barin gado, Godwin Obaseki na ci gaba da buɗe ayyukan da ya kammala yayin da yake shirin miƙa mulki
  • Obaseki ya bayyana cewa ya gamsu da ayyukan da ya yi wa al'umma a mulkinsa, inda ya ce ya cika alƙawurran da ya ɗauka
  • Nan da wasu ƴan kwanaki Obaseki zai sauka daga kan madafun iko, ya miƙa mulki ga zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya ce ya gamsu matuka da ayyukan da ya yi wa al'ummar jihar Edo yayin da yake haramar barin ofis.

Ya ce ya yi ayyuka masu muhimnanci a rayuwar al'umma waɗanda suka kunshi bunkasa ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki ga gina ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Wani bom ya tarwatse da mutane a babbar kasuwa a Najeriya, an rasa rayuka

Gwamna Godwin Obaseki.
Gwamna Godwin Obaseki ya ce ya gamsu da ayyukan da ya yi wa al'umma kusan shekaru 8 da hawa mulki Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Obaseki ya ce wadannan ayyuka da ya yi sun inganta rayuwar jama'a tare da dora jihar kan turbar ci gaba da bunkasar tattalin arziki, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Obaseki ya buɗe ayyuka a Edo

Gwamnan mai barin gado ya bayyana haka ne a wurin buɗe wasu sababbin ayyukan da gwamnatinsa ta kammala a Edo ranar Talata.

Gwamma Peter Mbah na jihar Enugu, tsohon gwamna kuma sanatan Sakkwato ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal da wasu manyan kusoshi sun halarci kaddamar da ayyukan.

Wasu daga cikin ayyukan da aka kaddamar sun hada da Kwalejin Fasaha ta Benin da wasu hanyoyin cikin kwalejin da ke da tsayin kilomita 12 da sauransu.

Gwamnan Edo ya ce ya cika alƙawaurrra

A wurin buɗe kwalejin fasaha a Benin, Obaseki ya ce gwamnatinsa ta dawo da fatan jama’a, ta sake gina tattalin arzikin Edo, tare da tallafawa matasa da ba su aiki.

Kara karanta wannan

Bayan masifar yan bindiga, wasu gungun miyagu daban sun sake bulla a Sokoto

"Wannan wani aiki ne da na ɗora ma kaina alhakin yi saboda lokacin da na fito takarar gwamna a zangon farko a 2016, muna fuskantar kalubale, yaranmu ba su son zuwa makaranta."
"Yayin kamfe na yi alkawarin dawo da fatan al'umma kuma na yi abin da ‘yan siyasa ba su saba yi ba, na yi alkawarin samar da ayyukan yi sama da 200,000, wanda yanzu mun wuce hakan."

- Godwin Obaseki.

EFCC ta kama hadiman gwamnan Edo

A wani rahoton, kun ji cewa EFCC ta kama Akanta Janar na jihar Edo, Julius O. Anelu da wasu jami'ai hudu da ke da alhakin fitar da kudi daga asusun gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta kama mutanen ne domin hana fitar da kudi yayin da wa'adin Gwamna Obaseki ke dab da karewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262