2027: Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Faɗi Ma'anar Sunan 'T-Pain' da Ake Kiran Tinubu
- Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Doyin Okupe ya ce ƴan Najeriya da kansu za su sake zaben Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Okupe ya ce sunan T-Pain da aka laƙabawa shugaban ƙasa na nufin radaɗi na wani lokaci, wanda zai wuce kuma mutane su warke
- Tsohon daraktan kamfen Peter Obi ya ce akwai yarjejeniya a ƙasa kan tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce ‘yan Najeriya za su sake zaben shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.
Mista Okupe ya bayyana cewa ƴan Najeriya da kansu zs su tallata Tinubu kuma su zaɓe shi ya ƙarisa shekaru takawas a kan madafun iko.
Doyin Okupe, tsohon daraktan kamfen Obi/Datti ya faɗi haka ne a shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi ikirarin cewa akwai yarjejeniyar da ba a rubuta ba game da tsarin karba-karɓa tsakanin Kudu da Arewacin Najeriya.
Yadda Tinubu zai yi tazarce a 2027
Okupe ya ce tsohon shugaban kasa Buhari “bai yi abin kirki ba” duk da haka ya shafe shekaru takwas a mulki kuma yanzu Tinubu na yin abin da ya dace shi ma a bari ya yi takwas.
"Wuƙa da dama na hannun ƴan Najeriya, su za su yanke shawara kuma na san suna da hankali da sanin ya kamata.
"Idan Bola Tinubu ya bamu haske kafin 2027, idan ya warware wannan matsalar man fetur da matsalar yunwa daga yau zuwa lokacin zaɓe, mutane da kansu za su ce Tinubu kawai suke so.
Ma'anar T-Pain da ake kiran Tinubu
Okupe ya ce laƙabin T-Pain da ƴan Najeriya suka jinginawa Tinubu a soshiyal midiya “yana nufin ciwo na ɗan lokaci wanda zai zama alheri ga ƙasa."
Ƴan Najeriya dai na fama da haihawar farashin da ba a taba ganin irinsa ba, kudin wuta ya nunka sau huɗu tunda Tinubu ya karɓi mulki a 2023.
Tinubu ya umarci a saki kananan yaran Kano
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yaran da aka tsare saboda zanga-zangar yunwa.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamban 2024
Asali: Legit.ng