Gwamna Ya Kara Yi Wa PDP Illa, Tsohon Ɗan Majalisa da Wasu Jiga Jigai Sun Koma APC

Gwamna Ya Kara Yi Wa PDP Illa, Tsohon Ɗan Majalisa da Wasu Jiga Jigai Sun Koma APC

  • Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya karɓi tsohon ɗan majalisa da wasu kusoshin PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC
  • Jiga-jigan sun shiga APC ne a wurin yakin neman zaɓen Gwamna Aiyedatiwa a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas
  • A ranar 16 ga watan Nuwamban da muke ciki INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamna a Ondo, Aiyedatiwa zai nemi tazarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Ondo sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki ana shirye-shiryen zaben gwamna a watan Nuwamba.

Tsohon ɗan majalisa, wanda ya wakilci mazaɓar Akoko ta Arewa maso Gabas/Arewa maso Yamma a majalisar wakilai, Stephen Olemija na cikin masu sauya sheƙar.

Kara karanta wannan

APC ta mayar da martani ga gwamna kan shirinsa na neman kujerar Tinubu a 2027

Tawagar kamfen gwamnan Ondo.
Gwamnan Ondo ya karbi wasu manyan kusoshin PDP a wurin kamfe Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Hakan na kunshe a wata sanarwa da gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan jiga-jigan PDP sun koma APC

Tsohon ɗan majalisar, Hon. Olemija ya sauya sheka ne tare da wasu manyan ƙusoshin PDP da tsofaffin shugabanni a mazaɓar.

Daga cikin waɗanda suka bi sahun tsohon ɗan majalisar har da Lekan Bada, tsohon ciyaman na Akoko ta Arewa maso Yamma da wani jigo, Momoh Mufu.

Olemija ya ce zai yi wuya jam’iyyar PDP ta samu goyon bayan jama’a a zaben gwamnan da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Gwamna Aiyedatiwa ya karɓi mutane a APC

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya karbi jiga-jigan masu sauya sheƙar zuwa APC da jirgin yakin neman zaɓensa ya dura ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu

Da yake karɓar masu sauya sheƙar, Gwamna Aiyedatiwa wanda shi ne ɗan takara a inuwar APC, ya ce gwamnatinsa za ta jawo kowa a jiki idan ta samu nasara.

Gwamnan ya jaddada cewa zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen tafiya da kowa ba tare da nuna wariya ba matukar ya samu nasara a zaɓe mai zuwa.

Gwamnan Ondo ya gana da Malamai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya yi wata ganawa da shugabannin Musulunci yayin da zaben jihar ke kara matsowa.

Malaman addinin Musulunci a jihar Ondo sun ce kamar yadda suka goyi bayan Bola Tinubu za su kara goyon bayan Aiyedatiwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262