APC Ta Mayar da Martani ga Gwamna kan Shirinsa na Neman Kujerar Tinubu a 2027

APC Ta Mayar da Martani ga Gwamna kan Shirinsa na Neman Kujerar Tinubu a 2027

  • APC mai mulki ta tankawa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo wanda ke shirin neman kujarar Shugaba Tinubu a 2027
  • Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka ya ce maimakon a ga Makinde na kokarin inganta rayuwar mutanen Oyo, ya koma kwashe kudinsu don tallata kansa
  • Morka ya yi ikirarin cewa duk wannan surutun da aka ji gwamnan Oyo na yi shure-shure ne kawai da ba zai hana mutuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC ta kasa ta caccaki Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo kan surutun da yake yi a ƴan kwanakin nan yana sukar gwamnatin Bola Tinubu.

APC ta yi ikirarin cewa gwamnan yana waɗannan surutai ne domin ɗauke hankalin jama'a daga gazawarsa da kuma kare burinsa na takarar shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

Shugaban APC da Gwamna Makinde.
APC ta tankawa gwamna Makinde kan burinsa na karawa da Tinubu a 2027 Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Seyi Makinde
Asali: Facebook

Leadership ta tattaro cewa Makinde na ci gaba da faɗi tashin neman tsayawa takara a inuwar PDP, inda ya ɗauri ɗamar karawa da Bola Tinubu a zaɓe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma zargi APC da hannu a rikicin cikin gida da ke faruwa a PDP da sauran jam'iyyun adawa.

2027: APC ta tankawa Gwamna Makinde

Da take martani, APC ta ce duk da gwamnan na da ƴancin tsayawa takara, amma yadda ya maida hankalinsa kacokan kan lamarin illa ce ga mutanen Oyo.

Jam'iyya mai mulki ta ce al'umma sun zabi Makinde a matsayin gwamna ne don ya masu aiki, ba don ya kwashe kudinsu ya koma kamfen neman takara ba.

APC ta faɗi haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Felix Morka ya fitar yau Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, hukumar INEC ta yi magana kan rikicin Majalisar dokokin jihar Ribas

Morka ya ce a wani taro da aka yi kwanan nan a Ibadan, gwamnan jihar Oyo ya zargi APC da haddasa rigingimun da ke faruwa a jam’iyyarsa ta PDP da sauran jam’iyyun adawa.

APC ta maida martani ga gwamnan Oyo

"Makinde ya gaza nuna cewa shi nagartaccen shugaba ne, shiyasa abin kunyar da ya yi a matsayin gwamna ya hana shi sukuni kuma ya zubar masa da mutunci a idon jama'a.
"Maimakon buƙatun waɗanda suka zaɓe shi su zama abin da ya fi ba fifiko, sai aka ga ya maida hankali wajen kwashe dukiyar talakawa don cimma burinsa na takara a 2027."

- Felix Morka.

APC na shirin karɓe Kusu maso Yamma

A wani labarin an ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan zaɓen jihar Ondo da ke tafe.

Ganduje ya bayyana cewa APC za ta ƙwace yankin Kudu maso yamma domin ƙara ƙarfin da take da shi kafin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262