An Samu Hayaniya a Majalisa, Sanata Ya Yaba Kyawun Minista, Akpabio Ya Gargade Shi
- An samu hayaniya a Majalisar Dattawa yayin tantance Ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya nada a makon da ya gabata
- Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya gargadi wani sanata kan yaba kyawun Bianca Ojukwu da ake tantancewa
- Akpabio ya ja kunnen sanatan inda ya ce ya mayar da hankali kan takardunta tun da ba ta saka tana da kyau a takardun ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ja kunnen Sanata saboda zubar da girmansa yayin tantance Ministocin Bola Tinubu.
Akpabio ya gargadi Sanata Osita Ngwu kan yabon kyawun Minista da ake tantancewa, Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu.
Sanata ya kyasa da kyawun Minista a Majalisa
Channels TV ta ce Akpabio ya nuna damuwa kan yadda sanata ya kauce hanya da ya yi magana kan kyawunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan kiran Bianca kyakkyawa lokacin da aka zo tantance ta a yau Laraba 30 ga watan Oktoban 2024.
Sai dai Akpabio ya ce Ministar da ake tantancewa ba ta saka a cikin takardunta tana da kyau ba saboda haka ya mayar da hankali kan takardunta.
"Ka mayar da hankali kan takardunta, ka manta da maganar kyawunta, ba ta saka a cikin takardunta cewa ita kyakkyawa ba ce."
- Godswill Akpabio
Sanata ya janye kalamansa kan Minista, Bianca
Wannan lamari tsakanin Akpabio da Sanata Ngwu ya jawo sanatoci a Majalisar sun fashe da dariya kafin daga bisani a samu natsuwa a Majalisar.
Daga bisani Sanata Ngwu janye maganar inda ya cigaba da yabon irin gudunmawar da Bianca ta bayar da sauran abubuwa da suka shafe ta.
An yi ce-ce-ku-ce kan shigar Akpabio masallaci
Kun ji cewa yan Najeriya sun yi ta korafi bayan ganin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a cikin masallacin Juma'a.
Wasu da suka tofa albarkacin bakinsu sun fara tambayar menene dalilin zuwan Akpabio cikin masallaci a matsayinsa na Kirista.
Hakan ya biyo bayan haduwar jiga-jigan Najeriya daga kowane bangare da kuma jam'iyyu a cikin masallacin Abuja a wani daurin aure.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng