Majalisar Dattawa Ta Waiwayi Sababbin Ministocin da Tinubu Ya Naɗa, Bayanai Sun Fito
- Majalisar dattawa ta gama shirin fara tantance sababbin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a gwamnatinsa
- Hadimin shugaban kasan kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado ya ce waɗanda aka naɗa sun fara kai takardunsu ga majalisa
- Shugaba Tinubu dai ya yi garambawul a majalisar zartaswa, inda ya kori ministoci shida sannan ya naɗa wasu sababbi 7
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta fara shirye-shiryen tantance sababbin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Basheer Lado, ya tabbatar da cewa sababbin ministocin sun fara bin matakan doka.
Ya ce ministocin guda bakwai sun fara kai takardun da ke kunshe da cikakkun bayanansu ga majalisar dattawa gabanin fara tantance su, in ji Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe majalisa za ta tantance ministocin?
Za a fara tantance su ne a ranar Talata, 29 ga Oktoba, 2024, a zauren majalisar dattawa da ke birnin tarayya Abuja.
A wata sanarwa da Basheer Lado ya fitar a daren ranar Litinin ya bayyana cewa tuni wadanda aka nada suka mikawa majalisar dukkan wasu takardu da ake buƙata.
Hakan wani ɓangare ne na aikin tantancewar da ƴan majalisar dattawan za su yi bayan Tinubu ya tura masu sunayen sababbin ministocin.
"Kamar yadda sashi na 147 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, majalisar dattawa ke da alhakin tantancewa da tabbatar da naɗin ministocin," in ji Basheer.
Jerin sababbin ministocin da za a tantance
Ministocin da shugaban ya naɗa sun hada da Dr Nentawe Yilwatda, ministan harkokin jin kai da rage talauci da Muhammadu Maigari Dingyadi, ministan ƙwadago.
Sauran sun ƙunshi Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu, ƙaramin ministan harkokin waje. Dr Jumoke Oduwole, ministar masana'antu da kasuwanci Idi Muktar Maiha, Ministan Dabbobi
Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, karamin ministan gidaje da kuma Dr Suwaiba Said Ahmad, karamar Ministar Ilimi, kamar yadda Vanguard ya ruwaito.
Akpabio ya yabawa gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarinta.
Ya ce lalacewar tattalin arzikin Najeriya ta samo asali ne daga gwamnatocin baya, ba a wannan gwamnatin da ke mulki ba.
Asali: Legit.ng