APC Ta Rikice da Sarakunan Gargajiya Suka Yi Murabus, Sun bi Layin Sanata
- Yayin da rigimar jam'iyyar APC ke kara ƙamari a jihar Sokoto, wasu sarakunan gargajiya sun yi murabus daga sarauta
- Sarakunan gargajiya sun fito ne daga yankin Sokoto da Gabas inda Sanata Ibrahim Lamido ke wakilta a Majalisar Tarayya
- Hakan ya biyo bayan samun matsala tsakanin sanatan da shugabannin jam'iyyar APC a jihar kan rashin tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Wasu sarakunan gargajiya a Sokoto ta Gabas sun yi murabus daga sarautar da suke rike da su.
Gamayyar sarakunan sun dauki wannan mataki ne domin bin Sanata Ibrahim Lamido ana tsaka da rigimar APC.
Sokoto : Sarakuna sun yi watsi da gwamna
Sarakunan gargajiya sun bayyana haka ne a yau Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024 a Sokoto, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarakunan sun nuna goyon bayansu ga sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Gabas da ke da matsala da shugabannin APC.
Suka ce sun dauki matakin tube rayukansu ne da bin sanatan kan korarin dakile matsalar tsaro a yankunansu.
Wasu daga sarakunan da suka yi murabus
Daga cikin wadanda suka ajiye rawunan nasu akwai Ubandoman Gatawa da Danmalan Ubandawaki da Salihu Katukan Gobir da Isah Haruna da Dangaladima Bashar.
Sai kuma Hassan S Fada da Yakubu Maigari da Malam Haruna da dagacin kauyen Kumbuli, Alhaji Ibrahim Gatawa da Mu’azu Mohammed Gatawa da sauran sarakunan masu yawa.
"Kowa ya sani Sanata Lamido ya kawo yan sa kai na CJTF kamar yadda aka yi a Maiduguri domin yakar yan bindiga a Isa da Sabon Birni."
"Tabbas ana cigaba da samun nasarori kan yaki da ta'addanci yayin da al'umma ke rayuwa cikin salama."
- Cewar sanarwar
Rigimar APC ta sake daukar sabon salo a Sokoto
Kun ji cewa rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta.
Jam'iyyar ta dade da rabewa gida biyu inda aka raba tafiya tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Samata Ibrahim Lamido.
Hakan ya biyo bayan zargin Sanata Wamakko da cin hanci da wasu yan jam'iyyar ke cewa yana bata musu suna.
Asali: Legit.ng