Kano: Hukumar KANSIEC Ta Mika Takardun Shaidar Cin Zabe ga Zababbun Ciyamomi 44

Kano: Hukumar KANSIEC Ta Mika Takardun Shaidar Cin Zabe ga Zababbun Ciyamomi 44

  • Hukumar KANSIEC ta mika takardun shaidar cin zabe ga sababbin ciyamomin kananan hukumomi 44 da aka zaba ranar Asabar
  • Shugaban hukumar zaben, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ya ce tsarin dokar zabe ce ta dorawa KANSIEC alhakin mika takardun
  • Legit Hausa ta rahoto gwamnan Kano, Abba Yusuf ya ce an gudanar da sahihin zabe irinsa na farko a tarihin zaben ciyamomin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) ta mika takardun shaidar cin zabe ga sababbin ciyamomin kananan hukumomi 44 da aka zaba.

Shugaban hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayar da takardun shaidar cin zaben a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Ku amince da shan kaye,' Abba ya aika sako ga 'yan adawa bayan zaben Kano

Hukumar KANSIEC ta yi magana yayin mika takardun cin zabe ga zababbun ciyamomin Kano
Kano: Hukumar KANSIEC ta mika takardun shaidar cin zabe ga zababbun ciyamomi 44. Hoto: Saifullahi A Bala
Asali: Facebook

KANSIEC ta ba da takardun cin zabe

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar ta ce jam’iyyar NNPP ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 44 da na kansiloli 484 a zaben da aka yi ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a lokacin da yake bayar da takardun cin zabe, Malumfashi ya ce:

"Hukumar za ta aiwatar da aikin bayar da takardar shaidar cin zabe ga zababbun ciyamomi da kansiloli a matsayin halastattun shugabannin kananan hukumominsu.
“Bisa ga tsarin gudanar da zabe, hukumar KANSIEC na da alhakin bayar da takardun shaidar cin zaben ga zababbun shugabannin."

Abba zai rantsar da sababbin ciyamomi

Farfesa Malumfashi ya ce daga yanzu zababbun ciyamomin na da hurumin halartar dukkanin ayyukan da ya shafi kananan hukumomin da suke jagoranta.

Legit Hausa ta fahimci cewa nan ba da jimawa ba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da sababbin ciyamomi da kansilolin a gidan gwamnati da ke Kano.

Kara karanta wannan

Hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar hukumar a ranar Asabar, Malumfashi ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali kananan hukumomin jihar.

Abba ya magantu kan zaben ciyamomi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga 'yan adawa da su amince da shan kaye a zaben ciyamomin jihar da aka kammala.

Gwamna Abba ya shaida cewa hukumar zaben jihar KANSIEC ta yi kokari matuka wajen ganin ta gudanar da sahihin zabe na farko irinsa a tarihin zaben ciyamomi a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.