'Ku Amince da Shan Kaye,' Abba Ya Aika Sako ga 'Yan Adawa bayan Zaben Kano
- Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya yi magana kan zaben ciyamomi da na kansiloli da hukumar zaben jihar (KANSIEC) ta gudanar
- Abba Yusuf ya ce an gudanar da sahihin zabe kuma yana da yakinin wadanda aka zaba za su yi shugabanci na gari ga al'ummarsu
- Jim kadan bayan kada kuri'arsa a karamar hukumar Gwalme, gwamnan ya ce sun dauki matakan kare jihar daga rikice-rikice
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya yaba da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar 44 cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya bayyana jin dadinsa da goyon bayan da shugabannin hukumar zaben wasu makotan jihohi suka bayar na sanya ido a zaben.
Abba ya magantu kan zaben ciyamomi
Mai girma Abba ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kada kuri'arsa a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa zaben da aka gudanar a unguwanni 484 a fadin kananan hukumomi 44, ya kasance mafi inganci a tarihin Kano.
Ya ba da tabbacin cewa wadanda aka zaba za su biya bukatun jama’a kuma gwamnatinsa za ta tabbatar da kyakkyawan shugabanci.
"An yi zabe na adalci" - Abba
Gwamnan ya yabawa shugaba da ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) kan yadda suka tabbatar da gudanar da “zabuka na gaskiya da adalci”.
Jaridar The Punch ta ruwato mai girma Abba ya ce:
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya yaba da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar 44 cikin kwanciyar hankali.
"Mun ga abin da ya faru a Ribas, don haka mun dauki matakan da suka dace don ganin ba a samu irin wannan lamarin a Kano ba."
Gwamna Yusuf ya kuma bukaci ‘yan adawa da su amince da shan kaye, saboda irin goyon bayan da jam’iyyarsa ke da shi na masu kada kuri’a.
NNPP ta lashe dukkanin zaben ciyamomi
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar KANSIEC ta bayyana cewa jam'iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 44 da kansiloli 484 na jihar Kano.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar KANSIEC da ke Kano, inda ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng