'Zan Hada Kai da Arewa': Asari Dokubo Ya Yi Nadamar Bin Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Yi Masa

'Zan Hada Kai da Arewa': Asari Dokubo Ya Yi Nadamar Bin Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Yi Masa

  • Alhaji Asari Dokubo ya bayyana irin nadamar da ya yi wurin goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 da aka gudanar a Najeriya
  • Dan gwagwarmayar ya ce ya kashe makudan kudi wanda har sai da ya karar da kudin asusun bakinsa saboda Tinubu
  • Dokubo ya sha alwashin haɗaka da yan Arewa a 2027 inda ya ce Yarbawa sun yaudari yan kabilar Ijaw kan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan gwagwarmaya, Alhaji Asari Dokubo ya fadi yadda Bola Tinubu ya yaudare shi a siyasa.

Dokubo ya ce ya kashe makudan kudi da ba za su misaltu ba wurin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2027: Manyan yan siyasar Arewa sun fara hada kai, suna ganawa kan tumbuke Tinubu

Asari Dokubo ya yi nadamar bin Tinubu, zai hada kai da Arewa
Asari Dokubo ya sha alwashin haɗaka da Arewa bayan nadamar bin Bola Tinubu a 2023. Hoto: Dokubo Asari, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

2027: Dokubo ya shirya haɗaka da Arewa

Alhaji Dokubo ya bayyana haka ne a cikin wani sabon faifan bidiyo da ya karfe kafofin sadarwa da Vanguard ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asari Dokubo ya ce a yanzu a shirye take domin hada kai da yan Arewa kan zaben 2027 da za a yi a Najeriya.

Dokubo ya ce ya kwashe dukan kudin da ke cikin asusun bakinsa domin ba da gudunmawa ga Tinubu a 2023.

Sai dai ya ce duk wannan gudunmawa da ya bayar, Tinubu ya watsa masa kasa a ido inda ya yaudare shi, cewar rahoton Punch.

Dokubo ya fadi yaudarar Tinubu a 2023

"Ina neman afuwa ga dattawanmu, ba su yi kuskure ba da suka hada tafiya da Arewa, mu ma yanzu matasa za mu hada kai da su."
"Daga yau zan fara aiki da yan Arewa, za mu hada kai, Tinubu ya yaudare ni bayan karar da kudi na gaba daya domin yi masa kamfe."

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

"Tinubu da na sani a baya, ba shi ne yanzu ba, zamu cigaba da yaɗawa cewa Arewa ce kadai zata tafi da mutanen Ijaw."

- Asari Dokubo

Dokubo ya ce ba za su sake aiki tare da Yarbawa ba saboda sun yaudare su, ya ce sun sadaukar da rayukansu amma a banza.

Yan Arewa sun fara neman tuge Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa wasu manyan yan siyasa a Arewacin Najeriya sun fara ganawa domin maye gurbin Bola Tinubu a 2027.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikinsu akwai wasu gwamnoni da suka yi nadamar goyon bayan Tinubu a 2023 saboda halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.