Hukumar Zaɓe Ta Sanar da Sakamakon Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Kano
- Jam'iyyar NNPP ta samu nasarar lashe zaben kananan hukumomin jihar Kano da aka yi ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2027
- Hukumar zaɓen Kano mai zaman kanta (KANSIEC) ce ta sanar da haka bayan kammala tattara sakamako a hedkwatarta da ke cikin birni
- Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya miƙa godiya ga malamai, jam'iyyu, sarakuna da sauran waɗanda suka ba da gudummuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano watau KANSIEC ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomin da aka yi yau Asabar.
Hukumar KANSIEC ta bayyana cewa jam'iyyar NNPP ta samu nasarar lashe dukkan kujerun ciyamomi 44 da kansiloli 484 na jihar Kano.
An yi zaɓe cikin lumana a jihar Kano
Shugaban Hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar KANSIEC da ke Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da nasara kuma mutane sun ba da haɗin kai yadda ya kamata, channels tv ta kawo.
Sani Lawan Malumfashi ya miƙa sakon godiya ga masu ruwa da tsaki waɗanda ya ce sun ba da gudummuwa wajen samun nasarar zaɓen cikin lumana.
Shugaban KANSIEC ya godewa malamai, sarakuna, jam'iyyu, mayasa maza da mata da sauran al'umma bisa goyon bayan da suka bayar a lokacin zaɓe.
NNPP ta samu nasara a dukkan kujeru
“Hukumar zaɓe tana matukar godiya ga al’ummar jihar Kano bisa hadin kai, addu’o’i da kuma goyon bayan da suka bayar a wannan zaɓe."
"Yadda zaben ya gudana cikin lumana ya nuna cewa mutane sun yi na'am da sahihanci da ingancin zaben. Jam'iyyun siyasa shida ne suka fafata, AA, AAC, ACCORD, ADC, APM da NNPP.
"Jam'iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da na kansiloli 484 da aka fafata a zaɓen."
- Sani Lawan Malumfashi.
Gwamna Abba ya amince da wasu ayyuka
A wani rahoton kuma kun ji cewa a zaman da aka yi ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba 2024, gwamnatin jihar Kano ta yanke wasu muhimman hukunci.
Majalisar zartarwa ta amince da wasu ayyuka da za su ci biliyoyin kudi domin inganta rayuwar mutanen jihar Kano.
Asali: Legit.ng