Sanata Ndume Ya Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Ƙara Korar Wasu Ministoci daga Aiki
- Sanata Mohammed Ali Ndume ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa garambawul din da ya yi a gwamnatinsa
- Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya buƙaci Tinubu ya sake haska majalisar zartaswa domin akwai sauran ministocin da ya kamata a kora
- Ya kuma baiwa shugaban ƙasar shawarar ya haɗa taron tattalin arziki domin lalubo mafita da wannan halin da ƙasa ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara korar ministoci.
Sanata Ndume, wanda ya saba tsage gaskiya komai ɗacinta a jam'iyya mai mulki, ya buƙaci Tinubu ya kara tankaɗe da rairaya a majalisar zartaswa.
Ali Ndume ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar sanar Asabar, 26 ga watan Oktoba a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya yabawa Shugaba Tinubu
Ndume ya ayyana garambawul ɗin da Tinubu ya yi da kafa ma’aikatar raya yankuna don kula da dukkan hukumomin raya shiyyoyin kasar nan a matsayin ci gaba.
Ɗan majalisar dattawan ya ce:
"Har yanzu a akwai sauran aiki domin akwai sauran ministocin da ya kamata a sallama."
Yadda Tinubu ya yi garambawul
Idan baku manta ba a ranar Laraba da ta gabata, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul, inda ya tsige ministoci shida, sannan ya naɗa wasu bakwai.
Hakazalika shugaban ƙasar ya sauyawa wasu ministoci 10 wuraren aiki duƙ a yunƙurinsa na cika alƙawurran da ya ɗauka.
Ndume ya ba Tinubu shawara kan tattalin arziki
Sanata Ndume, tsohon mai tsawatarwa a majalisar dattawa ya buƙaci Tinubu ya kira taron tattalin arziki domin lalubo mafita daga halin da ake ciki a ƙasar nan.
Ya ce waɗanda ya dace su jagoranci taron sun haɗa da tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala da tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili.
Tinubu ya umarci hadimansa su rage ayari
A wani labarin kuma Bola Tinubu ya umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya su rage motocin da ke cikin ayarinsu.
Shugaban kasar ya kuma umarci ministoci da shugabannin hukumomin su rage yawan jami'an tsaronsu zuwa jami'ai biyar.
Asali: Legit.ng