Kwankwaso Ya Gana da Ƴan Majalisar Tarayya na NNPP, An Nemi Mutum 3 An Rasa
- Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da ƴan majalisar tarayya na jam'iyyar a gidansa da ke Abuja
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan majalisa uku sun kauracewa zaman, wanda ana ganin hakan na da alaƙa da rikicin da ya ɓarke a NNPP
- Sanata Kawu Sumaila na cikin waɗanda suka ki halartar taron saboda zargin ana nuna masu wariya wajen tafiyar da harkokin NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da ƴan majaisar tarayya na jam'iyyar NNPP a jihar Kano.
Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke fama da rikicin ciki wanda ya raba kawunan wasu daga cikin kusoshin NNPP.
Hadimin Kwankwaso na fannin kafafen sada zumunta, Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan ganawar jagoran NNPP na ƙasa da ƴan majalisar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron wanda aka gudanar a gidan Kwankwaso na Abuja, an yi shi ne don magance rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP reshen Kano.
Ƴan majalisa 3 sun kauracewa zama da Kwankwaso
Sai dai ba a ga fuskokin mutum uku daga cikin ƴan majalisar a wurin taron ba, Sanata Suleiman Kawu Sumaila, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, da Aliyu Sani Madakin Gini
Rashin ganin fuskokin kusoshin uku ya kara tabbatar da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa akwai tsama a jam'iyyar NNPP.
An tattaro cewa Aliyi Madakin Gini ya daina sa jar hula, alamar ƴan Kwankwasiyya, sannan ba a gan shi a wurin muhimman tarukan NNPP ba.
NNPP na fama da rikicin cikin gida
Rurum da Sanata Kawu Sumaila sun nuna ɓacin ransu kan yadda Kwankwaso ya maida su saniyar ware wajen fitar da ƴan takarar ciyaman da kansiloli a Kano.
Wannan ƙorafin ya sa aka fara tunanin suna shirin sauya sheka daga NNPP musamman ma saboda saɓanin da ka samu kan dokar masarautar Kano.
Rashin halartar wadannan ‘yan majalisar ya fara tayar da kura a tsakanin magoya bayan jam’iyyar.
Sauran ‘yan jam’iyyar NNPP daga Kano, irin su Sanata Rufa’i Sani Hanga da Tijjani Abdulqadir Jobe, sun halarci zaman a Abuja.
Wani jigon NNPP, Malam Sa'idu Abdu ya ce bai yi mamakin rashin ganin Sanata Kawu Sumaila da Alhassan Rurum a wurin ganawa da Kwankwaso ba.
Ƴa shaidawa Legit Hausa cewa dama tun asali sun shigo NNPP ne domin neman mulki kuma sun samu, shiyasa daga baya suka fara ɓullo da son rai.
Jigon ya ce:
"Su a tunaninsu komai za a yi a NNPP dole sai da su, daga baya ma suka fara adawa da Mai gida, ka ga hakan ba zaya saɓu ba.
"Ina tabbatar maka da cewa jam'iyyar NNPP a dunƙule take babu wata ɓaraka, duk masu tada jijiyoyin wuya kwangila suka karɓo, wanda in sha Allahu ba za su ci nasara ba."
Kwankwaso ya yi magana kan ilimi
A wani rahoton kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya ce gudummawar da ya bayar a ɓangaren ilimi na gina jami'o'i biyu na faranta masa rai.
Jagoran NNPP ya bayyana cewa a dukkan ayyukan da ya yi lokacin yana matsayin gwamnan Kano, ya fi jin daɗin gina jami'o'in nan
Asali: Legit.ng