Halin da Mutane Ke Ciki a Kano Yayin da Zaɓen Kananan Hukumomi Ya Kankama
- Yayin da zaɓe ya kankama a jihar Kano, rahotanni sun nuna mutane sun yi biyayya ga umarnin taƙaita zirga-zirga
- A yau Asabar 26 ga watan Oktoba aka tsara yin zaɓen kananan hukumomi a jihar Kano duk da umarnin kotun tarayya
- Bayanai sun nuna cewa galibin shagunan ƴan kasuwa a kulle suke, tituna kuma babu yawan ababen hawa a cikin kwaryar birnkn Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa mutane sun yi biyayya ga dokar taƙaita zirga-zirga yayin da zaɓen kananan hukumomi ya kankama.
Tun farko gwamnatin Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a faɗin ƙananan hukumomi 44 daga ƙarfe 12 na tsakar dare zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin yau Asabar.
Kwamishinan yaɗa labarai, Baba Ɗantiye ya ce an sa wannan doka ne domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da zaɓe cikin lumana, Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta amince a yi zaɓen Kano
Hakan na zuwa ne bayan babbar kotun Kano ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta watau KANSIEC damar gudanar da zaben kananan hukumomi yau.
Kotun ta kuma yi fatali da duk wani yunƙuri da jam'iyyun siyasa suka yi da nufin hana yin zaɓen, ta sahalewa KANSIEC gudanar da aikinta.
Mai shari’a Sanusi Ma’aji wanda ya jagoranci shari’ar, ya yanke hukuncin cewa KANSIEC na da ikon gudanar da zabubbukan kananan hukumomi 44 na jihar bisa doka.
Halin da ake ciki a Kano yau Asabar
A rahotannin da muka samu da safiyar yau Asabar, mazauna Kano suun yi biyayya ga dokar da gwamnatin Kano ta sanya ta taƙaita zirga-zirga.
Galibin shaguna na kulle, hanyoyi kuma babu mutane sosai yayin da aka fara shriye-shiryen fara kaɗa kuri'a a zaben da aka tsara yau Asabar, 26 ga Oktoba.
Sanusi Abdullahi, wani ɗan Kano ya shaiɗawa Legit Hausa cewa bai fita kasuwa ba saboda za a yi zaɓe yau Asabar a jihar.
"Gaskiya mutane sun ba da hadin kai, zaɓe ya gudana cikin lumana, muna fatan waɗanda suka samu nasara su yi abinda ya dace.," in ji shi.
Gwamna Abba ya yi magana kan zaɓe
A wani rahoton na daban gwamnatin Kano ta ce ba za ta bar wasu tsirarun mutane su kawo cikas ga zaben kananan hukumomi a ranar Asabar ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a yi zabe a Kano duk da kotu ta haramta gudanar da zaben bisa wasu dalilai da ta zayyana
Asali: Legit.ng