Kotu Ta Jiƙawa Jam'iyyar NNPP Aiki Awanni Kafin Zaben Kananan Hukumomi a Ƙano
- Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta kori ƴan takarar kujerar ciyaman 44 na jam'iyyar NNPP a zaben kananan hukumomin da za a yi
- Alkalin kotun ya umarci hukumar zaɓen jiha watau KANSIEC ta akrbi sunayen ƴan takarar daga tsagin NNPP karkashin Ɗanhatu Shehu Usman
- Haka nan kotun ta hana jami'an tsaro ba da kariya a rumfuna matuƙar ba canza sunayen ƴan takara kamar yadda ta umarta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Yayin da ake shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a gobe Asabar a Kano, babbar kotun tarayya ta kori ƴan takarar NNPP 44.
Kotun wanda ke zamanta a Kano ta kori dukkan ƴan takarar ciyaman na jam'iyyar NNPP a zaɓen da aka shirya yi ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024.
Mai shari'a Simon Amobeda ne ya yanke wannan hukunci ranar Jumu'a a ƙarar da Injiniya Muhammad Babayo da tsagin NNPP suka shigar, Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta sauya ƴan takarar NNPP
Mai Shari'a Amobeda ya umarci hukumar zaɓen Kano (KANSIEC) ta karbi sabon sunayen ƴan takarar ciyaman daga tsagin NNPP da Dalhatu Shehu Usman ke jagoranta.
Alkalin ya ce dole ne hukumar KANSIEC ta amince da jerin sunayen ‘yan takarar da masu kara suka gabatar.
Ƙarar ta ƙunshi hukumar zabe ta ƙasa (INEC), KANSIEC, Sufeto Janar na ‘yan sanda, da daraktan hukumar DSS a matsayin wadanda ake tuhuma na 1, 2, 3 da 4.
An hana INEC ba da kayan zaɓe
"Kotu na umartar INEC da ka da ta ba hukumar zaɓen Kano kayan zaɓe domin gudanar da zaɓen da aka tsara ranar 26 ga watan Oktoba, 2024," in ji alkali.
Kotun ta kuma hana jami’an tsaro bayar da kariya a rumfunan zabe idan zaben ya gudana ba tare da sabunta jerin sunayen ‘yan takara ba, in ji The Nation.
Zaben Kano: KANSIEC ta gama shiri
A wani rahoton kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano ta ce dama a shirye ta ke wajen gudunar da zaben ciyamomi ba tare da cikas ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ya fadi haka jim kaɗan bayan hukuncin babbar kotun jiha da ya sahale a yi zabe.
Asali: Legit.ng