Ganduje Ya Sake Cika Baki, Ya Fadi Jihar da APC Za Ta Kwace
- Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tarɓi wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Rivers zuwa cikin jam'iyyar
- Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar ta shirya karɓe tsarin siyasar jihar Rivers mai arziƙin man fetur da ke a yankin Kudu maso Kudu
- Kalaman na Ganduje na zuwa ne bayan ya yi irinsa a jihar Ondo, da ya ce APC za ta ƙwace sauran jihohin da ke a Kudu maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam’iyyar ta shirya karɓe tsarin siyasar jihar Rivers.
Abdullahi Ganduje ya cika baki kan cewa jihar mai arzikin man fetur ta jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ce.
Ganduje ya tarɓi dan takara zuwa APC
The Nation ta ce Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da kwamitin gudanarwa na ƙasa na APC (NWC), ya karɓi ɗan takarar gwamnan Rivers na jam’iyyar AA, Dakta Dawari Ibietela George a zaɓen 2023 zuwa cikin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tarbar tsohon ɗan majalisar zuwa APC, Ganduje ya bayyana cewa shigowarsa cikin APC zai taimakawa jam'iyyar samun ƙuri'un da za su ba ta damar ƙwace jihar.
Shugaban na APC ya bayyana cewa za a gudanar da gagarumin gangami domin tarbarsa zuwa jam'iyyar a hukumance tare da ɗumbin magoya bayansa.
"Muna farin cikin shigowarka cikinmu. Na san cewa kai gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya yi takara kuma ya ci zaɓe, sannan ka yi takara kuma ka yi rashin nasara."
"Saboda haka ka shirya mana. Jihar Rivers jiharmu ce. A jihar Rivers ka san muna buƙatar ƙuri'u masu ɗumbin yawa. Don haka Rivers ta shirya da zuwanmu, APC za ta mamaye Rivers gaba ɗaya."
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya gigita jam'iyyar PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana yankin da jam'iyyar APC za ta ƙwace.
Ganduje ya ce APC za ta ƙwace yankin Kudu maso Yamma ta hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng