PDP Ta Amince Damagum Ya Sauka, Za a Bayyana Sabon Shugaban Jam'iyya na Ƙasa

PDP Ta Amince Damagum Ya Sauka, Za a Bayyana Sabon Shugaban Jam'iyya na Ƙasa

  • Jagororin PDP na shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara laluben wanda ya kamata su miƙa a matsayin sabon shugaban jam'iyya na ƙasa
  • Rahotanni sun ce gwamnoni da sauran masu ruwa da tsakin PDP sun amince Umar Damagum ya sauka daga shugabanci a taron NEC
  • Ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024 za a yi taron majalisar zartaswan PDP ta ƙasa watau NEC mai hurumin zartar da hukunci kan NWC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Masu ruwa da tsaki sun fara laluben wanda zai maye gurbin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum gabanin taron majalisar zartaswa watau NEC.

Jam'iyyar PDP ta shirya taron kwamitin zartaswa NEC wanda ke da alhakin zartar da hukunci musamman kan shugabanci a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da jiga jigai sun gano abin da zai hana PDP ƙwace mulki daga Tinubu a 2027

Umar Damagum.
PDP ta cimma matsaya, an fara duba wanda zai maye gurbin Umar Damagum Hoto: @OfficialPDP
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa tuni kwamitin zartarwa na Arewa ta Tsakiya (ZEC) ya fara laluben wanda ya kamata ya karɓi shugabancin PDP daga shiyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arewa ta Tsakiya za ta kawo shugaban PDP

A cewar wasu majiyoyi, tattaunawa ta yi nisa kuma ana sa ran za a yanke hukunci a hukumance bayan zaben gwamnan jihar Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Jagororin PDP na Arewa ta tsakiya karkashin gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, sun tabbatar da shirinsu na zaɓo sabon shugaban jam'iyya domin kammala wa’adin Iyorchia Ayu.

PDP ta ba Arewa ta Tsakiya damar gabatar da sabon shugabanta ne a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda aka yi ranar Talata a masaukin gwamnan Bauchi da ke Abuja.

Jam'iyyar PDP ta amince Damagum ya sauka

Ɓangarorin da suka halarci zaman sun haɗa da kwamitin gudanarwa NWC, kungiyar gwamnonin PDP, da kwamitin amintattun jam'iyya watau BoT.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Daga karshe an fadi yankin da zai samar da shugaban jam'iyyar na kasa

Sauran waɗanda aka gani a taron sun haɗa da ƴan majalisar tarayya na PDP da kuma ƙungiyar tsofaffin gwamnoni, inji Vanguard.

Majiyoyi daga taron sun tabbatar da cewa gwamnoni sun amince Damagum ya bar mukaminsa, kana a maye gurbinsa daga shiyyar Arewa ta tsakiya.

PDP ta hango matsala gabanin zaɓen 2027 

A wani rahoton kuma gwamnoni da shugabannin PDP na kasa sun nuna damuwa kan rikicin cikin gida da ya ƙi karewa a jam'iyyar adawar.

Sun ce matukar ba a binne duk wani saɓani ba, rikicin ka iya kawo cikas a kokarin jam'iyyar PDP na komawa kan madafun iko a 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262