Zaben Ondo: Gwamnan APC Ya Fadi Makomar Jam'iyyar PDP a Jihar

Zaben Ondo: Gwamnan APC Ya Fadi Makomar Jam'iyyar PDP a Jihar

  • Gwamnan Ondo ya taso jam'iyyar PDP a gaba gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar, 16 ga watan Nuwamban 2024
  • Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar ta mutu domin duk ƙusoshinta sun dawo APC mai mulki
  • Ɗan takarar gwamnan na APC ya buƙaci mutanen jihar da su kaɗa ƙuro'unsu ga APC domin ta samu nasara a zaɓen da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa kuma ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan jihar Ondo, ya yi wa jam'iyyar PDP shaguɓe.

Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta mutu murus gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.

Kara karanta wannan

"Za ka sha mamaki," Gwamna ya maida martani mai zafi ga shugaban APC, Ganduje

PDP ta mutu a Ondo
Gwamna Aiyedatiwa ya ce PDP ta mutu a Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Gwamnan Ondo ya ce PDP ta mutu

Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana haka ne a wajen yaƙin neman zabensa a Igbobini, Kiribo Igbotu, da sauran garuruwan ƙaramar hukumar Ese-Odo da ke jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Aiyedatiwa ya buƙaci mutane da su yi magana da ƙuri’unsu ta hanyar zaɓar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta mutu a jihar don haka bai kamata su ɓata ƙuri'unsu wajen zaɓenta ba, rahoton The Punch ya tabbatar.

"Ina so ku yi amfani da ƙuri'ar ku wajen korar sauran jam'iyyun siyasa. Kamar yadda kuka sani, duk manyan ƙusoshin jam’iyyar PDP, yanzu suna tare da mu."
"Mun yagalgala laimar babbar jam’iyyar adawa ta PDP. A wannan zaɓe mai zuwa, ƙuri’ar ku ta kasance ta APC ce."

- Gwamna Lucky Aiyedatiwa

Kara karanta wannan

"Ban tsoron hukumar EFCC": Gwamnan PDP ya fadi dalili

Gwamnan PDP ya gargaɗi Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa PDP za ta tumurmusa APC mai mulki a zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi a watan Nuwamba.

Gwamnan ya ce babbar jam'iyyar adawar za ta ba shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Lucky Aiyedatiwa mamaki ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel