"Za Ka Sha Mamaki," Gwamma Ya Maida Martani Mai Zafi ga Shugaban APC Ganduje

"Za Ka Sha Mamaki," Gwamma Ya Maida Martani Mai Zafi ga Shugaban APC Ganduje

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya mayar da martani ga shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje da Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  • Makinde ya ce PDP za ta ba Ganduje da Gwamna Aiyedatiwa mamaki a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba
  • Tun farko dai Ganduje ya ce APC ta gama shirin karɓe jihohin Kudu maso Yamma yayin da Aiyedatiwa ya yi ikirarin PDP ta zama gawa a Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa PDP za ta tumurmusa APC mai mulki a zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi a watan Nuwamba.

Gwamnan ya ce babbar jam'iyyar adawa za ta ba shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Lucky Aiyedatiwa mamaki ranar 16 ga watan gobe.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko ya kere gwamnoni, an ba shi lambar yabo ta kasa da kasa a Faransa

Shugaban APC da Gwamna Makinde.
Gwamna Makinde ya lashi takobin dawo da Ondo hannun PDP a zaben 16 ga watan Nuwamba Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Seyi Makinde
Asali: Facebook

Kalaman Ganduje da Gwamnan Ondo

Leadership ta rahoto cewa Ganduje ya yi iƙirarin cewa APC za ta karɓe mulkin duka jihohin Kudu maso Yamma bayan lashe zaɓen gwamnan Ondo mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, gwamnan Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa jam'uyyar PDP ta mutu murus jihar, ba za ta iya taɓuka komai ba.

Da yake mayar da martani kan waɗannan kalamai, Makinde ya ce har yanzun PDP na nan da ƙarfinta kuma ta shirya lashe zaɓen gwamnan da za a yi a Ondo.

Makinde ya faɗi haka ne a Ikare Akoko, hedikwatar karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas lokacin da ya jagoranci kwamitin kamfen PDP zuwa yankin Akoko.

Gwamna Makinde ya maida martani ga Ganduje

A ruwayar Tribune, gwamnan wanda shi ne jagoran PDP a Kudu maso Yamma ya ce:

Kara karanta wannan

'Kirista dan Kudu,' Tsagin PDP ya fadi wanda zai shiga takara a 2027

"Ina tabbatar maku cewa mutanen Kudu maso Yammacin Najeriya idonsu a buɗe yake musamman a nan jihar Ondo, ku duba gangamin da jama'a suka yi a nan, abin sha'awa.
"A ranar 16 ga watan Nuwamba, jama'a za su gaya masa (Ganduje) da yaren da zai gane cewa Ondo da Kudu maso Yamma na PDP ne, suna ganin abu ne mai sauƙi.
"Kuna da damar faɗin duk abin da kuke so amma al'ummar Ondo za su yi magana da babbar murya a zaben da za a yi ta yadda kowa da kowa a ƙasar nan zai fahimta."

NNPP ta shirya karɓe mulkin Ondo

A wani rahoton kuma jam'iyyar NNPP ta na ganin ita ce za ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya bayyana yakinin da su ke da shi a lokacin kaddamar da dan takararsu, Olugbenga Edema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262