Bayan Shafe Shekaru a Kasan Kwankwaso, Ganduje Ya Fadi Illar Zama Mataimakin Gwamna

Bayan Shafe Shekaru a Kasan Kwankwaso, Ganduje Ya Fadi Illar Zama Mataimakin Gwamna

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci kawo sauyi a tsarin dokar mataimakan gwamnoni
  • Shugaban jam'iyyar APC ya ce akwai bukatar yin garambawul da samar da doka kan ayyukan mataimakan gwamnoni
  • Ganduje ya koka kan yadda ba su da wani iko ko aiki na musamman daga kundin tsarin mulki sai abin da gwamna ya ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan rawar da mataimakan gwamnoni ke takawa.

Ganduje ya bukaci samar musu da wata rawa da za suke takawa ta musamman domin inganta alaka da iyayen gidansu.

Ganduje ya ba da shawara kan rawar da mataimakan gwamnoni za su taka
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bukaci gyaran fuska kan rawar mataimakan gwamnoni a Najeriya. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Ganduje ya bukaci gyara alakar gwamna, mataimakinsa

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya yi fallasa, ya fadi abin da ke firgita gwamnoni a mulki

Shugaban APC ya fadi haka ne yayin wani taro da kungiyar tsofaffin mataimakan gwamnoni (FFDGN) a Abuja, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce inganta mataimakan gwamnonin da gyara alakarsu da gwamnoni zai kawo sauyi a dimukraɗiyya.

Tsohon gwamnan Kano ya yabawa kungiyar kan yadda suka hada kawunansu tun bayan kafa ta, The Guardian ta ruwaito.

Ganduje ya fadi illar kasancewa mataimakin gwamna

"Zama mataimaki yana da wuyar sha'ani, ko kai mataimakin gwamna ne ko na shugbana kasa ko kuma na shugaban makaranta duka daya ne."
"Idan kana da shugaban, dole watarana zai kwanta rashin lafiya ko kuma ya yi mutuwar bazata, dole za a samu wani da zai cigaba da jagoranci."
"Kamar mataimakin shugaban kasa yana da ayyukansa a kundin tsarin mulki, amma ban da mataimakin gwamna shi sai abin da mai gidansa ya ba shi."

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamna a Arewa ya yi amai ya lashe kan shugabancin PDP na ƙasa

- Abdulla Ganduje

Ganduje ya ce ya kamata a rika raba ayyuka a tsakani saboda taimakon juna inda ya ce bai dace shugaba ya yi aiki shi kadai ba.

Za a yanke hukunci kan zargin Ganduje

Kun samu labarin cewa yayin da ake shari'a kan zargin shugaban APC, Abdullahi Ganduje da cin hanci, kotu ya shirya yanke hukunci.

Babbar kotun jihar Kano ta sanya 20 ga watan Nuwambar 2024 a matsayin ranar raba gardama kan dukkan zargin.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Ganduje da matarsa da wasu mutane kan karkatar da biliyoyin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.