Zaben Kananan Hukumomi Zai Lakume Kudi, Gwamna Zai Kashe Naira Biliyan 2

Zaben Kananan Hukumomi Zai Lakume Kudi, Gwamna Zai Kashe Naira Biliyan 2

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ga jihar Ogun ta ce za a kashe makudan kudi a zaben kananan hukumomi
  • Shugaban hukumar, Babatunde Osibodu ya ce an yi kasafin kashe akalla sama da Naira biliyan biyu don yin nasarar yin zabe
  • Ya bayyana cewa ba haka kawai aka samu karin farashin ba, inda ya ce an samu matsaloli kamar karin farashin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun - Ana shirin gudanar da zaben kananan hukumomi mai tsadar gaske yayin da hukumar zaben jihar ta Ogun ta ware biliyoyi domin zaben.

Shugaban hukumar zaben jihar, Babatunde Osibodu ya bayyana cewa an ware sama da Naira biliyan biyu wajen tabbatar da zaben a cikin nasara.

Kara karanta wannan

"Ko da jami'an tsaro ko babu, za a yi zabe:" Majalisar dokokin Kano ga kotu

Zaben
Za a kashe sama da Naira biliyan 2 a zaben Ogun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa za a kashe kudaden ne domin muhimman ayyukan da za su tabbatar da an yi zaben yadda ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a kashe kudin zaben Ogun

Babatunde Osibodu ya bayyana cewa za a kashe N1bn domin zirga-zirga yayin zaben da za a yi ranar 16 Nuwamba, 2024.

Shugaban hukumar zaben ya kara da cewa za a karbo kayayyakin zabe daga hukumar INEC a kan Naira miliyan 200.

Me ya kawo tsadar zaben Ogun?

Mista Babatunde Osibodu ya dora alhakin tsadar kayayyakin zabe da kudin mota a kan hauhawar farashi da tsadar fetur.

Ya kara da cewa a shekarar 2021, an bugo rajistar zabe daga hukumar INEC a kan Naira miliyan 15, amma a wannan jikon zai kai Naira miliyan 200.

"Akwai lam'a a baben kananan hukumomi:" OCCEN

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, kotu ta tsige shugaba da manyan jami'an hukumar zaben jihar Kano

A zantawarsa da Legit, Shugaban kungiyar karfafawa mutane gwiwa da shiga harkokin dimokuradiyya, Kwamared Abdularak Alkali ya ce wannan almubazzaranci ne.

Shugaban kungiyar OCCEN ya ce har yanzu akwai sarkakiya a yadda ake gudanar da zaben kananan hukumomi ta fuskoki da dama.

Daga cikin inda ya ce ana samun matsala, Kwamred Alkali ya zargi gwamnatin tarayya da muzgunawa jihohin da ba jam'iyyarta ke mulki ba, cusa kudin zabe da kane-kane da gwamnatocin jihohi ke yi a sakamakon zaben.

Za a yi zaben kananan hukumomi

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin ji cewa majalisar dokokin Kano ta jaddada matsayar gwamnatin jihar ta tabbatar da an gudanar da zaben kananan hukumomi.

Wata babbar kotun tarayya ce dai ta yanke hukuncin da ke haramta gudanar da zaben da aka shirya yi a ranar Asabar, 26 Oktoba, 2024 saboda saba dokar nada shugaban KANSIEC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.