Damagum: Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe kan Shugabancin PDP na Ƙasa

Damagum: Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe kan Shugabancin PDP na Ƙasa

  • Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya amince da shugabancin Umar Damagum
  • Da yake jawaci a taron da PDP ta shirya, aBala ya ce kansu a haɗe yake kuma za su daƙile yunkurin maida Najeriya hannun jam'iyya ɗaya
  • Wannan na zuwa ne bayan wani ɗan tsagin PDP da ke goyin bayan gwamnan Bauchi ya shigar da ƙara gaban babbar kotun Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Bayan shan matsin lamba ta kowace kusurwa, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi amai ya lashe, ya amince da shugabancin Umar Damagum a PDP

Tun farko tsagin PDP da ke goyon bayan gwamnan ya shigar da ƙara gaban kotu, ya nemi izinin gudanar da taron majalisar zartaswa NEC.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Kungiyar gwamnonin PDP ta fadi gaskiya kan shigar da kara kotu

Damagum da Gwamnan Bauchi.
Gwamnan Bauchi ya yi amai ya lashe, ya amince da shugabancin Umar Damagum a PDP Hoto: @OfficialPDPNig, @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito cewa wani mai suna Imam Auwal ne ya shigar da ƙara a babbar kotun Zamfara, ya roki soke haramcin tsige muƙaddashin shugaban PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala ya amince da Damagum

Amma a ranar Talata, shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya yi mubayi'a ga shugabancin Damagum a wani taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar a Abuja.

Gwamna Bala ya amince da shugabanncin Damagum a wurin taron wanda aka shirya domin sasanta ƴan kwamitin gudanawar NWC da suka rabu gida biyu.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnoni biyar daga cikin 13 ne suka halarci taron jiya Talata da daddare a masaukin gwamnan Bauchi a Abuja, in ji Channels tv.

Waɗanda aka hanga a wurin taron a lokacin haɗa wannan rahoton su ne Gwamna Bala na Bauchi, Dauda Lawal na Zamfara, Caleb Mutfwang na Filato, Sim Fubara na Ribas da Ademola Adeleke na Osun.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da gwamna kan mutuwar mutane 181, bayanai sun fito

Dalilin taron masu ruwa da tsakin PDP

A jawabin maraba da ya yi gabanin fara taron, Gwamna Bala Mohammed ya ce maƙasudi ɗaya tal za a tattauna a taron shi ne warware saɓani.

Gwamnan Bauchi ya ce:

"Wannan taron PDP ne, ba taron gwamnoni ko na masu ruwa da tsaki ba ne, abu ɗaya muka tasa a gaba. Kamar yadda kuke gani kan mu a haɗe yake karkashin jagorancin Umar Damagum."
"Ba za mu bari a maida Najeriya ƙasa mai jam'iyya ɗaya ba, za mu baje dabarun da muka koya tun 1999 domin samar da wani zaɓi ga ƴan Najeriya."

Ortom ya musanta rabuwar kawuna a PDP

A wani rahoton kuma Samuel Ortom ya bayyana cewa babu wani ɓangare a jam'iyyar PDP ta kasa kamar yadda ake yaɗawa a baya-bayan nan.

Tsohon gwamnan jihar Benuwai ya ce Umar Damagum ne sahihin shugaban PDP na riko, babu wani tsagi da ya ɓalle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262