Jam'iyyar PDP Ta Sake Dage Taron NEC, Ta Bayanai Dalili

Jam'iyyar PDP Ta Sake Dage Taron NEC, Ta Bayanai Dalili

  • Jam'iyyar PDP mai adawa ta sake ɗage taron majalisar zartaswa na ƙasa (NEC) da ta shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoban 2024
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ɗage taron zuwa Nuwamban 2024
  • An cimma wannan matsayar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a daren ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A karo na uku jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ta dage taron majalisar zartaswa na ƙasa (NEC).

Taron wanda tun da farko aka shirya gudanar da shi a watan Agusta, an mayar da shi zuwa watan Satumba. Daga nan aka mayar da shi ranar 24 ga watan Oktoba, sannan yanzu an ɗage shi zuwa 28 ga Nuwamba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Daga karshe an fadi yankin da zai samar da shugaban jam'iyyar na kasa

PDP ta dage taron NEC
Jam'iyyar PDP ta dage taron NEC zuwa watan Nuwamba Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

An yanke hukuncin ɗage taron ne a babban taron ƙungiyar gwamnonin PDP, kwamitin amintattu (BoT), kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da tsofaffin gwamnoni, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da aka fara da ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata, an kwashe awanni ana gudanar da shi, rahoton jaridar Daily Trust ta tabbatar da wannan.

Meyasa jam'iyyar PDP ta ɗage taron NEC?

Da yake karanta sanarwar bayan taron, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed, ya ce sun yanke shawarar ne domin ba shugabannin jam’iyyar damar maida hankali kan zaɓen gwamnan Ondo da ke tafe.

"An ɗage taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC), da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024.
"An ɗage taron ne domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta shiga zaɓen gwamnan Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024 tare da haɗin kai da ƙarfin da ake buƙata wajen kawar da gwamnatin APC a jihar."

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamna a Arewa ya yi amai ya lashe kan shugabancin PDP na ƙasa

- Bala Mohammed

Gwamnonin PDP sun je kotu kan taron NEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar adawa PDP ya ɗauki sabon bayan da wasu gwamnoni suka shigar da ƙara gaban kotun kan taron majalisar zartaswa, NEC.

Tsagin PDP da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ke jagoranta ya nemi kotu ta ba da umarnin gudanar da taron NEC na PDP ta ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng