Taron NEC: Rikicin PDP Ya Ɗauki Sabon Salo, Gwamna Ya Jagoranci Kai Kara kotu

Taron NEC: Rikicin PDP Ya Ɗauki Sabon Salo, Gwamna Ya Jagoranci Kai Kara kotu

  • Tsagin PDP karkashin gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya shigar da kara gaban kotu kan taron majalisar zartaswa watau NEC
  • Masu karar sun roƙi kotu ta ba da umarnin gudanar da taron NEC wanda ake sa ran zai maida hankali kan kujerar shugaban PDP na ƙasa
  • Har yanzu dai ana ci gaba da taƙaddama kan kujerar Umar Damagum, muƙaddashin shugaban PDP bayan sauke Iyorchia Ayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar adawa PDP ya buɗe sabon babi da wasu gwamnoni suka shigar da ƙara gaban kotun kan taron majalisar zartaswa NEC.

Tsagin PDP da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ke jagoranta ya nemi kotu ta ba da umarnin gudanar da taron NEC na PDP ta ƙasa

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, kotu ta tsige shugaba da manyan jami'an hukumar zaben jihar Kano

Gwamna Bala Mohammed.
Tsagin gwamnan Bauchi ya nemi umarnin kotu na shirya taron majalisar zartaswa ta PDP Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: UGC

Kamar yadda The Nation ta tattaro, an shigar da wannan kara ne a gaban babbar kotun jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damagum: Rikicin jam'iyyar PDP ya kara tsananta

Mai shari'a Salim Ibrahim ne zai jagoranci zaman shari'a kan wannan kara da tsagin Gwamna Bala Muhammed, shugaban kunguyar gwamnonin PDP ya shigar.

Tawagar masu ƙarar ta buƙaci a soke hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Abuja da ta haramta tsige muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum.

Yadda gwamnonin PDP suka rabu 2

Idan ba ku manta ba kungiyar gwamnonin PDP ta dare gida biyu, wasu na goyon bayan Damgum ya ci gaba da shugaban jam'iyya wasu kuma na adawa da hakan.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne jagoran waɗanda ke kokarin sauke Damagum, tare da ɗora wanda zai maye gurbinsa daga Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko ya kere gwamnoni, an ba shi lambar yabo ta kasa da kasa a Faransa

A ɗaya ɓangaren kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne jagoran waɗanda ke goyon bayan Damagum ya ci gaba zama a kujararsa.

A halin yanzu tsagin Bala Mohammed ya kai ƙara kotu domin a kira taron majalisar zartaswa NEC mai alhakin yanke makomar Umar Damagum, rahoton Daily Post.

Gwamnonin PDP sun ɗagawa Damagum ƙafa

A wani rahoton kuma gwamnonin PDP sun dauki manyan matakai yayin da rikicin jam'iyyar ya kara ƙamari wanda ya kai ga an samu rabuwar kawuna

An rahoto cewa gwamnonin sun amince Umar Damagum ya ci gaba da zama matsayin shugaba zuwa ranar 24 ga Oktobar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262