Ganduje Ya Gigita PDP, Ya Fadi Yankin da Jam'iyyar APC Za Ta Kwace

Ganduje Ya Gigita PDP, Ya Fadi Yankin da Jam'iyyar APC Za Ta Kwace

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan zaɓen jihar Ondo da ke tafe
  • Ganduje ya bayyana cewa APC za ta ƙwace yankin Kudu maso Ƙudu domin ƙara ƙarfin da take da shi kafin zaɓen 2027
  • Shugaban na APC ya ce ba zai faɗi sirrin APC ba na ƙwato jihohin Oyo da Osun waɗanda ke hannun jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana yankin da jam'iyyar APC za ta ƙwace.

Ganduje ya ce APC za ta ƙwace yankin Kudu maso Yamma ta hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya feɗe gaskiya kan rigimar shugabancin PDP na ƙasa

Ganduje ya fadi shirin APC
Ganduje ya ce APC za ta kwace yankin Kudu maso Yamma Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ganduje ya yi taro a Ondo

Jaridar Daily Trust ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar APC zuwa taron masu ruwa da tsaki a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wajen taron, Ganduje ya ce jam’iyya mai mulki na aiki tuƙuru domin ganin ta ƙara ƙarfi kafin zaɓen 2027 mai zuwa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ganduje ya faɗi shirin APC kan jihohin PDP

Shugaban na APC ya kuma jaddada cewa dole ne jihohin Oyo da Osun su kasance ƙarƙashin jam’iyyar APC domin ƙara goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu yake da shi, musamman a Kudancin ƙasar nan.

Ganduje ya bayyana cewa APC ba za ta bayyana dabarun da za ta bi wajen samun nasara a jihohin yankin ba.

Kara karanta wannan

NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso ta buɗe ƙofa, za a yi wa Tinubu taron dangi a 2027

Ya ce zaɓen gwamna da za a yi a jihar Ondo mai sauƙi ne a wajen APC, inda ya ƙara da cewa ɗaukacin shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa sun nuna goyon bayansu ga gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa.

"A wannan yankin, dole ne mu bayar da kaso 100% don goyon bayan APC. Saboda haka jihar Ondo, dole ne ta kasance kan gaba, sauran jihohin biyu Oyo da Osun za mu ƙwato su, amma ba zan faɗi sirrinmu ba."

- Abdullahi Umar Ganduje

APC ta lashe zaɓe a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC mai milki ta lashe zaɓe a dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Jam'iyyar APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta gudanar ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng