Rigimar APC Ta Sake Dagulewa da Sanata Wamakko da Lamido Suka Ja Ɓangarensu

Rigimar APC Ta Sake Dagulewa da Sanata Wamakko da Lamido Suka Ja Ɓangarensu

  • Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta
  • Jam'iyyar ta dade da rabewa gida biyu inda aka raba tafiya tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Samata Ibrahim Lamido
  • Hakan ya biyo bayan zargin Sanata Wamakko da cin hanci da wasu yan jam'iyyar ke cewa yana bata musu suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rikicin jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya dauki sabon salo a yan kwanakin nan.

Duk da nasarar da jam'iyyar ta samu a jihar daga PDP, hakan ya zamo mata kalubale da take fama da shi.

Jam'iyyar ta sake shiga matsala a jihar Sokoto
Rigimar APC a jihar Sokoto ta sake rabewa tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Ibrahim Lamido. Hoto: Senator Aliyu Magatakarda Wamakko, Senator Ibrahim Lamido.
Asali: Facebook

Matsalar APC ta sake dagulewa a Sokoto

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun watsa taron jam'iyya, sun sace mataimakin shugabanta na kasa

Leadership ta ce an yi ta kokarin rufa-rufa kan rigimar jam'iyyar amma yanayin sai kara fitowa yake daga 'ya'yanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta dare gida biyu inda kowane bangare ke neman iko kan jagorancinta a jihar watanni bayan gagarumar nasararta a zaben 2023.

Sanata Aliyu Wamakko da ke wakiltar Sokoto ta Arewa shi ya ke jagorantar daya bangaren sai kuma Sanata Ibrahim Lamido da ke wakiltar Sokoto ta Gabas a daya bangaren.

Musabbabin samun matsalar APC a Sokoto

Wasu rahotanni sun ce rigimar bata rasa nasaba da neman kwace ikon jam'iyyar a hannun Wamakko kan zargin cin hanci.

Wasu 'ya'yan jam'iyyar sun tabbatar da cewa zargin da ake yiwa Wamakko zai rika batawa APC suna.

An tabbatar da cewa Sanata Lamido na cigaba da samun goyon bayan yan jam'iyyar ciki har da mambobin Majalisar Tarayya daga jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya ƙara ƙamari, babban basarake a Arewa ya yi murabus daga sarauta

APC ta dare gida 2 a Sokoto

Kun ji cewa Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu zai iya fuskantar matsala bayan wasu daga cikin yan jam'iyyarsa ta APC sun daina goyon bayansa.

APC ta rabu, yayin da wasu daga cikin yan APC su ka ware kansu karkashin jagorancin Ibrahim Lamido domin kalubalantar gwamnan.

Tsagin Lamido ya bayyana cewa ba zai fita daga cikin APC ba, amma za su ware gefe guda domin ba su gamsu da yadda gwamnan ke mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.