Kaduna: APC Ta Lallasa PDP da Sauran Jam'iyyun Adawa a Zaben Ciyamomi
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta sanar da zaɓen shugabannin ƙananana hukumomin da aka gudanar a ranar Asabar
- Shugabar hukumar zaɓen ta bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 a zaɓen
- Hajara Mohammed ta kuma sanar da cewa APC ta lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen wanda jam'iyyun siyasa takwas suka fafata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Jam’iyyar APC ta lashe zaɓe a dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
Jam'iyyar APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta gudanar ranar Asabar.
Tashar Channels tv ta ce shugabar hukumar zaɓen jihar, Hajara Mohammed, ce ta sanar da sakamakon zaɓen a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta lallasa ƴan adawa a Kaduna
Hajara Mohammed ta ce jam'iyyun siyasa takwas ne suka fafata a zaɓen, inda APC ta samu kujerun ciyamomi 23 da na kansiloli 255, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Ta ƙara da cewa jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasara a ƙananan hukumomin da suka haɗa da Birnin-Gwari, Chikun, Igabi, Ikara, Jaba, Jema’a, Kachia, Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu.
Sauran ƙananan hukumomin da jam’iyyar APC ta lashe a cewar shugabar hukumar zaɓen sun haɗa da Kagarko, Kajuru, Kaura, Kauru, Kubau, Kudan, Lere, Makarfi, Sabon Gari, Sanga, Soba, Zango-Kataf da Zaria.
A ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba ne dai aka gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kaduna.
An yi yadda aka saba
Mahmud Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa bai yi mamaki ba domin ya san cewa APC ce za a ce ta lashe zaɓen.
Ya bayyana a inda ya ke zaɓe ma har bayan ƙarfe 2:00 na rana ko kayan zaɓen ba a kawo ba.
"Wannan zaɓen ai dama a shirye yake sun gama tsara abin su. Mu a wajenmu ko kayan zaɓen ba a kawo ba har bayan ƙarfe 2:00 na rana."
- Mahmud Auwal
Mutane sun yi biris da doka a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen Kaduna a ranar Asabar sun bijirewa dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya a faɗin jihar.
Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar ne domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar na ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.
Asali: Legit.ng