2027: Jam'iyyar LP na Aiki a Boye ga APC Mai Mulki? an samu karin bayanai

2027: Jam'iyyar LP na Aiki a Boye ga APC Mai Mulki? an samu karin bayanai

  • Jam'iyyar LP mai adawa a Najeriya ta musanta rade-radin cewa tana yiwa APC mai mulki aiki a boye
  • Jam'iyyar ta caccaki tsohon kusa a LP, Kenneth Okonkwo da shugaban NLC, Joe Ajaero kan yada karairayi
  • Hakan ya biyo bayan yada jita-jitar cewa shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure na yiwa APC aiki kan zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar LP ta yi martani kan zargin da ake yi mata da cewa tana yiwa APC aiki.

Jam'iyyar ta musanta rade-radin da ake yadawa inda ta ce ana neman bata martabarta ne kawai.

Jam'iyyar LP ta yi magana kan zargin yiwa APC aiki
Jam'iyyar LP ta ƙaryata labarin yiwa APC aiki a Najeriya. Hoto: Labour Party.
Asali: Facebook

Jam'iyyar LP ta caccaki shugaban NLC

Kara karanta wannan

"Na cancanta," Sanatan APC ya bayyana shirinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da LP ta wallafa a shafinta na X a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta caccaki tsohon jigonta, Kenneth Okonkwo da shugaban NLC, Joe Ajaero kan yada jita-jitar.

Har ila yau, jam'iyyar LP ta ce babu kamshin gaskiya kan zargin shugabanta, Julius Abure da alaka da APC.

LP ta nisanta yiwa APC aiki

"Ya zama dole jam'iyyar LP ta yi martani kan zargin da ake yadawa domin batawa shugabanninta suna."
"Bayan samun nasara a kotu, Kenneth Okonkwo da shugaban NLC suna zargin LP na yiwa APC aiki shiyasa take samun nasara."
"Wannan rade-radin da ake yadawa karya ne kula babu kamshin gaskiya kan lamarin, ana yi ne domin bata mata suka, LP jam'iyya ce mai zaman kanta."

- Cewar sanarwar

Kara karanta wannan

“Nan ba Legas ko Edo ba ce:” NNPP ta yi kurarin samun nasara a zaben Gwamna

Kotu ta tabbatar da Abure shugaban LP

Kun ji cewa Babbar kotun tarayya da ake zamanta a birnin Abuja ta yi hukunci kan taƙaddamar shugabanci da ta dabaibaye jam'iyyar Labour Party (LP).

Alƙalin kotun ya tabbatar da Barista Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa a hukuncin da ya yi a ranar Talata, 8 ga watan Oktoban 2024.

Mai shari'a Emeka Nwite ya umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta amince da Abure a matsayin halastaccen shugaban LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.