"Kuna da Damar Taimakon Ƴan Najeriya," Jigon APC Ya Dura kan Kwankwaso da Atiku

"Kuna da Damar Taimakon Ƴan Najeriya," Jigon APC Ya Dura kan Kwankwaso da Atiku

  • Tsohon kwamishina a Kano ya bayyana irin gudummuwar da ake bukata daga Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi
  • Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce lokaci ya yi da manyan ƴan siyasar za su jingine adawa, su taimaki ƴan Najeriya a halin da ake ciki
  • Jagoran ya yi wannan kalamai ne a lokacin da mutane ke fama da matsin rayuwa sakamakon manufofin gwamnatin APC mai ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kira ga manyan ƴan takara uku da suka kara da Bola Tinubu a zaben 2023 su jingine batun siyasa a gefe.

Musa Iliyasu, tsohon kwamishina kuma jigon APC a Kano ya buƙaci Peter Obi, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso su tallafi ƴan Najeriya a halin ƙuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Atiku, Obi da Kwankwaso.
Jigon APC ya bukaci Atiku, Obi da Kwankwaso su aje adawa a gefe Hoto: Atiku Abubakar, Mr. Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Abin da ake bukata daga Kwankwaso, Atiku, Obi

Ya ce maimakon sukar gwamnati mai ci, kamata ya yi manyan ƴan siyasar su ba da gudummuwa wajen magance yunwa da matsin rayuwa, The Nation ta kawo labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musa Iliyasu ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba, 2024 a birnin Kano.

Tsohon kwamishinan ya ce babu tantama ƴan Najeriya na cikin ƙuncin rayuwa amma kowa ya san irin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi.

Jigon APC ya caccaki manyan ƴan takara 3

Musa ya ce:

"Kamata ya yi mu ga suna ba da gudummuwa, su shiga layin masu kokarin kawo mafita maimakon su koma gefe suna adawa tare da sukar gwamnati.
"Wane irin gudummuwa suke badawa a rayuwar mutane a wannan mawuyacin hali?

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Gwamna Abba ya juyawa Kwankwaso baya kan mutum 2 a Kano

"Misali mu ɗauki Kwankwaso, me ya yi a mazaɓarsa da maƙwabta kamar Jigawa na yayewa magoya bayansa damuwa?
"Ba abin da yake yi, maimakon haka ma ya koma yana yaƙar gwamnatin da ya kafa a Kano."

"Muna bukatar haɗin kai" - Musa Iliyasu Kwankwaso

Jigon APC ya kuma gargaɗi Atiku Abubakar kan yawan sukar gwamnatin Tinubu, yana mai tambayarsa abin da ya yi na taimakon mutane a wannan hali.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ƙara da cewa Najeriya ta hau wani siraɗi mai wahala, wanda ke bukatar haɗa karfi da karfe wajen lalubo mafita, Tribune ta rahoto.

An fara hasashen nasarar APC a 2027

A wani labarin kuma masana sun fara sharhi kan yadda lamarin siyasar Najeriya ke gudana a halin yanzu da abin da zai iya faruwa a gaba.

Hakan na zuwa ne bayan an yawaita samun rikicin cikin gida a tsakanin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya a wannan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262