“Nan ba Legas ko Edo ba ce:” NNPP Ta Yi Kurarin Samun Nasara a Zaben Gwamna

“Nan ba Legas ko Edo ba ce:” NNPP Ta Yi Kurarin Samun Nasara a Zaben Gwamna

  • Jam'iyyar NNPP ta na ganin ita ce za ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024
  • Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya bayyana yakinin da su ke da shi a lokacin kaddamar da dan takararsu, Olugbenga Edema
  • Ya kara da zargin APC mai mulki a kasa da kokarin yin tazarce a kan kujerar shugabancin kasar har bayan babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar OndoJam’iyyar adawa ta NNPP ta bugi kirji a kan zaben gwamnan jihar Ondo da ke tafe a ranar 16 Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Anambra: INEC ta sanya lokacin gudanar da zaben gwamna, ta fadi shirin da ta yi

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya gargadi APC da cewa za a yi zaben Ondo bisa cancanta da tabbatar da zabin jama’ar jihar.

Zaben Ondo
NNPP ta ce dan takararta zai yi nasara a zaben gwamnan Ondo Hoto: Gbenga Edema Media
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban jam’iyyar ya zargi APC da kokarin cigaba da kakabawa jama’a yan takararta a zaben 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar NNPP ta hango nasara a zaben Ondo

Rahoton Nigerian Tribune ya tattaro cewa shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya ce mutanen Ondo za su zabi dan takarar jam’iyyarsa a zaben gwamnan jihar.

Ya bayyana haka ne a gangamin kaddamar da dan takarar gwamna a inuwar NNPP a jihar Ondo, Olugbenga Edema.

NNPP na son mutanen jihar Ondo su zabe ta

Ajuji Ahmed ya shawarci jama’ar Ondo su tabbatar da sun kadawa Olugbenga Edema kuri’a a zaben gwamna da za a yi ranar 16 Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso ta buɗe ƙofa, za a yi wa Tinubu taron dangi a 2027

Shugaban na NNPP ya sanar da mutanen Ondo cewa tuni su ka bijiro da wasu kudurori da za su taimaki jama’a tare da fitar da su daga cikin kangin da su ke ciki.

“APC ke haddasa rigima a jam’iyyu:” NNPP

A baya mun ruwaito cewa jam’iyyar NNPP ta yi zargin cewa APC ce kanwa uwar gami wajen haddasa rikicin cikin gida a jam’iyyun kasar nan, domin tarwatsa jam’iyyun kafin zaben 2027.

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ne ya yi zargin, ya kara da cewa APC ta haddasa rikice-rikicen ne domin ta kama kasa wajen samun nasara a babban zaben 2027 mai karatowa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.